CBN Ya Maida Martani Kan Rahoton Da ke Yawo Na Dakatar da Opay da Palmpay

CBN Ya Maida Martani Kan Rahoton Da ke Yawo Na Dakatar da Opay da Palmpay

  • CBN ya maida martani kan labarin da ke yawo a midiya wanda ya yi ikirarin ya dakatar da ayyukan bankunan Intanet 2, Opay da Palmpay
  • OPAY da PALMPAY suna cikin bankunan da babban bankin Najeriya ya baiwa lasisin aikin hada-hadar kuɗi ta Intanet
  • Shugabannin kamfanonin kuɗin guda biyu sun yi tsokaci kan labarin da ke yawo na dakatar da ayyukansu a Najeriya

Abuja - Babban bankin ƙasa (CBN) ya yi fatali da rahoton da ke cewa ya dakatar da ayyukan bankunan zamani na intanet, OPAY da PALMPAY, bayan gano suna da hannu a aikata damfara.

Premium Times ta rahoto cewa muƙaddashin kakakin CBN, Isah Abdulmumin, ya ce labarin karya ne kuma ya kamata 'yan Najeriya su yi watsi da shi.

Gwamnan CBN.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Asali: Getty Images

Daga ina rahoton ya samo asali?

Kara karanta wannan

Yan Jagaliya Sun Kaddamar da Hari a Ofishin APC dake Zamfara, Biyu Sun Tafi Lahira

A wata sanarwa da ta yaɗu a soshiyal midiya wacce aka jingina wa Abdulmumin, ta yi ikirarin cewa CBN ya gama shirin dakatar da ayyukan Kamfanonin hada-hadar kuɗin gudana biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan kasan kana amfani da manhajar OPAY, PALMPAY ko wasu daga cikin manhajojin China ko POS ɗinsu, ka daina zuba kuɗi da yawa a asusu ko ka daina amfani da su."
"CBN na gab da dakatar da ayyukan su saboda an gano cewa ana amfani da irin waɗannan Manhajojin wajen aikata damfara," inji Sanarwan.

Opay da Palmpay sun maida martani kan rahoton

Yayin martani kan rahoton, OPAY da Palmpay, sun yi falati da zancen inda suka bayyana cewa suna gudanar da ayyukansu bisa dokoki da ƙa'idojin CBN.

Opay ya yi bayani cewa labarin dake yawo cewa CBN zai dakatar aikinsa ba gaskiya bane kuma zai sauya akalar mutane.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

Haka zalika, Palmpay, ya bukaci ɗaukacin yan Najeriya da su yi watsi da wannan labarin da aka kirkira domin batar da tunaninsu.

OPAY da PALMPAY na cikin kamfononin hada-hadar kudi da ake kira da bankunan Intanet, waɗanda ke taimakawa mutane wurin biyan Bill da sauran mu'amalar da ta shafi kudi.

Bankuna Sun Bi Umarnin CBN Na Fitowa Aiki a Karshen Mako

A wani labarin kuma Bankuna sun fito aiki a ranakun karshen mako bayan umarnin babban bankin CBN

Sakamakon barazanar mamaye rassan CBN a jihohin Najeriya, babban bankin ya umarci bankunan kasuwanci su fito ranar Asabar da Lahadi su baiwa mutane kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262