Gwamnan Jihar Gombe Ya Aike Da Sakon Ta'aziyyar Sa Kan Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar
- Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta'aziyyar sa kan rasuwar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar
- Nasiru Nono ya rasu ne a wani mummunan haɗarin mota da ya auku akan titin hanyar Abuja-Keffi
- Gwamnan ya bayyana mamacin a matsayin mutumin kirki wanda ya zauna lafiya kowa sannan yayi masa addu'ar samun rahama a wajen Allah
Jihar Gombe- Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya nuna kaɗuwar sa kan rasuwar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Nasiru Nono. Rahoton Punch
Allah ya yiwa tsohon kakakin majalisar dokokin jihar rasuwa ne a ranar Alhamis a wani mummunan haɗari da ya auku a kan titin hanyar Abuja zuwa Keffi.
Yahaya ya nuna baƙin cikin sa kan samun labarin rasuwar mamacin a wata sanar da babban darektan watsa labarai na gidan gwamnatin jihar Ismaila Uba-Misilli, ya fitar.
Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara
Ya bayyana rasuwar tsohon ɗan majalisar a matsayin wani babban rashi wanda ba a iyalan sa kaɗai ya tsaya ba har da jihar da Najeriya gabaɗaya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace tsohon ɗan majalisar mutum ne mai ƙan-ƙan da kai wanda yake sananne ne wajen jajircewar kan ganin cewa ya kyautatawa mutanen mazaɓar sa da jihar gabaɗaya. Rahoton The Guardian
Gwamnan ya bayyana cewa tsohon kakakin majalisar ya gudanar da ayyukan sa cikin kula da takatsantsan da sanin yakamata yayin da yake shugabancin majalisar dokokin jihar, wanda hakan ya sanya abokanan aikin sa ke ganin mutuncin sa.
Sanarwar na cewa:
“A madadin gwamnati da al'ummar jihar Gombe, ina miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyalan mamacin, abokanan siyasar sa da al'ummar ƙaramar hukumar Yamaltu Deba."
“Ina addu'ar Allah ubangiji ya sanya mamacin a Aljannah Firdaus.”
Za Mu Hukunta Duk Musulmin Kano Da Muka Kama Yana Cin Abinci A Bayyane Yayin Ramadan, In Ji Hisbah
A wani labarin na daban kuma, hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta aike da wani muhimmin gargaɗi kan al'ummar jihar yayin da aka shiga wstan azumin Ramadan.
Hukumar ta aike da wannan gargaɗin ne kan masu cin abinci a bainar jama'a yayin da ake azumi.
Asali: Legit.ng