Yan Bindiga Sun Halaka Soja Da Raunata Wasu Daban A Jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindiga sun halaka wani soja tare da raunata wasu wani bata kashi da suka yi da sojoji
- Miyagun ƴan bindigan sun shammaci sojojin ne inda suka buɗe musu wuta ba zato ba tsammani
- Tsautsayi ya kuma gitta kan wani farar hula mazaunin ƙauyen da abin ya auku inda ya samu raunika
Jihar Kaduna- Ƴan bindiga sun halaka wani soja a yayin wani artabu a ƙauyen Akoti kusa da Kagarko a cikin jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sojoji uku da wani farar hula suka samu raunika a yayin harin.
Wani mazaunin ƙauyen, Yahaya Ubaidu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar tarhon ranar Laraba, yace harin ya auku ne da misalin ƙarfe biyar na yamma lokacin da sojojin suka yi musayar wuta da ƴan bindigan a ƙauyen Akoti.
Ya bayyana cewa an kira sojojin ne bayan ƴan bindigan sun sace shanu sama da 100 a ƙauyen Kasangwai dake makwabtaka da su inda suke wucewa ta cikin Akoti. Sojojin sun iso sannan aka fara musayar wuta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayi bayanin cewa sojojin da suka zo a cikin motoci biyu, ƴan bindigar shammatar su suka yi suka buɗe musu wuta, inda suka halaka ɗaya daga cikin su sannan suka jikkata wasu uku daban.
Ya cigaba da cewa:
"Harsashin da ƴan bindigan suka harba ya samu ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen da yake gudun neman mafaka, sannan yanzu haka yana asibitin koyarwa na jami'ar Abuja (UATH) dake a Gwagwalada."
Ya cigaba da cewa ƴan bindigan waɗanda suka samu galaba akan sojojin sun kuma ƙona ɗaya daga cikin motar sojojin sannan suka tafi da shanun.
Madakin Janjala, Samaila Babangida, ƴa tabbatar da aukuwar lamarin.
“Daga bayanan da na samu a safiyar yau, sojojin sun daga Kaduna domin ɗauke sojoji uku da suka samu raunika da gawar sojan da aka halaka." Inji shi
Ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba kan wannan lamarin da ya auku a jihar.
Yan Ta’addan ISWAP Sun Yiwa Dakarunsu da Sojojin Najeriya Kashe Jana’iza a Cikin Daji
A wani labarin na daban kuma, ƴan ta'addan ISWAP sun yi asara mai yawa a hannun dakarun sojojin Najeriya.
Ƴan ta'addan sun gudanar da jana'izar dakarun su da sojoji suka sheƙe.
Asali: Legit.ng