Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Abba Kyari Kan Rushe Tuhumarsa da Ke da Harkallar Kwaya
- Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya yi watsi da bukatar Abba Kyari na neman soke tuhumarsa da ake da harkallar kwaya
- Kyari da abokansa da ke gaban kotu sun nemi a tattara tuhume-tuhumen da ake musu tare da watsar dasu, kamar yadda lauyoyinsu suka gabatar
- Sun bukaci kotun da ta dakata da shari’arsu, inda suka ce ba a ladabtarsu a cikin gida ba daidai da ka’idar rundunar ‘yan sanda
FCT, Abuja – Babban kotun tarayya a Abuja ya yi watsi da bukatar Abba Kyari da abokan harkallarsa kan bukatar soke zarge-zargen da ke kansu game da harka da miyagun kwayoyi.
Wannan lamarin ya faru ne a ranar Laraba 22 ga watan Maris a gaban kotun, inda Kyari ya ce ya kamata a dakata da batun tuhumarsa kan kwaya tukuna, The Guardian ta ruwaito.
A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Emeka Nwite ya yi watsi da bukatar, inda yace kotun na da dama da ikon sauraran batutuwa da suka shafi harkallar kwaya, kamar yadda yazo a kundin dokar NDLEA.
Bukatar Kyari a gaban kotu
Channels Tv ta ruwaito cewa, alkalin ya kuma kara da cewa, sashe na 251 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kotun ikon sauraran irin wannan kara.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kyari ya shaidawa kotun cewa, shigo da batun gaban kotu ya yi wuri, inda yace NDLEA ta yi gaggawa a madadin ta bari a bincike shi a cikin gida; a hukumar ‘yan sanda.
Haka kuma ya shaidawa kotun cewa, tuni hukumar ‘yan sanda ta fara bincike game da lamarin kuma ta fara fitar da rahoto game da hakan.
A fahimtarsa, ya kamata a titsiye shi a gaban kotu ne bayan kammala binciken hukumar ‘yan sanda sabanin yadda aka yi a yanzu.
Kitimurmurar Kyari da NDLEA
Kyari, wanda tsohon jami’in dan sanda ne a runduna ta musamman ta IRT na fuskantar tuhumar NDLEA da hannu a harkallar miyagun kwayoyi.
An maka Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda hudu na IRT; ACP Sunday J. Ubua, ASP Bawa James, Sufeta Simon Agirgba da Sufeta John Nuhu a gaban babban kotun tarayya.
An ruwaito cewa, ana zarginsu da shigo da kayan maye na hodar iblis da yawansa ya kai kilo-giran 17.55.
A baya, wani ya yi bayanin yadda Abba Kyari ya yi masa alkawarin kudade masu yawa idan ya yiwa Bukola Saraki sharri.
Asali: Legit.ng