Tashin Hankali Yayin da Wasu ’Yan Bindiga Suka Kona Wata Babbar Kotu a Jihar Ebonyi

Tashin Hankali Yayin da Wasu ’Yan Bindiga Suka Kona Wata Babbar Kotu a Jihar Ebonyi

  • Rahoton da muke samu daga jihar Ebonyi ya bayyana yadda wasu ‘yan ta’adda suka kone kotu a jiya Talata 21 ga watan Maris
  • Sun kone dukkan takardu da abubuwa masu daraja a kotun, kamar yadda majiya ta tabbatar ga manema labarai a jihar
  • Ana yawan samun barnar ‘yan ta’adda a Kudu maso Gabas, kuma kone kayan gwamnati ya zama ruwan dare da ke yawan faruwa

Jihar Ebonyi - An ruwaito yadda wasu tsagerun ‘yan daba suka bankawa babban kotun Owutu-Edda da ke karamar hukumar Afikpo South ta jihar Ebonyi.

Oluchi Uduma, magatakardan kotun ne ta tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Owutu-Edda a ranar Laraba 22 ga watan Maris.

A cewarta, ‘yan daban sun mamaye kotun ne a ranar Talata, inda suka banka masa wuta nan take, rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yadda 'yan bindiga suka binne matar sarkn Fulani a Arewa bayan karbar kudin fansa

Yadda 'yan ta'adda suka yi barna a Ebonyi
Jihar Ebonyi mai fama da 'yan ta'addan Kudanci | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Uduma ta yi bayanin cewa, ginin kotun, takardun da ke ciki da sauran kayayyaki masu daraja gaba dayansu sun kone kurmus.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Chima Nkama, shugaban karamar hukumar Afikpo South ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa, an kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda.

Ba wannan ne karon farko na kotu ba

A watan Disamban 2022, nan ma wasu tsageru sun bankawa kotun majistare da ke garin Owerri a jihar Imo wuta, inda suka kone shi kurmus.

Lamarin ya faru ne sa’o’i kadan bayan da aka kone wani babban kotun da ke karamar hukumar Orlu duk dai a jihar ta Imo, Punch ta ruwaito.

Kone kotuna da sauran gine-ginen gwamna ya zama ruwan dare a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, akan zargin kungiyar ta’addanci ta IPOB da aikata barnar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

An sha samun lokuta mabambanta da ‘yan ta’addan ke kone ofishin ‘yan sanda, INEC ko dai wani wuri mai daraja haka kawai babu gaira babu dalili.

An hallaka ‘yan sanda a Taraba

A wani labarin, kun ji yadda sojoji suka hallaka wasu jami’an ‘yan sanda biyu da kuma jikkata biyu a wurin tattara sakamakon zabe.

Wannan lamarin ya haifar da hargitsi, har ta kai ga samun jinkiri a aikin tattara sakamakon zaben gwamnan jihar.

Zaben bana ya zo da matsaloli da yawa, ciki har da kashe-kashe a wasu yankuna daban-daban na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.