Yadda ’Yan Bindiga Suka Sheke Matar Sarkin Fulanin Rugan Ardo, Suka Binne Ta a Maboyarsu
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka hallaka matar basaraken Fulani a jihar Kaduna
- Sun kuma shaida cewa, ai tuni ma sun binne matar a cikin dajin da suke boye duk da sun karbi kudaden fansa masu yawa
- Wannan ba sabon abu bane a jihar Kaduna, ya sha faruwa a lokuta daban-daban, musamman a yankin Janjala na jihar Kaduna
Kagarko, jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun shaidawa iyalan sarkin Fulani na Rugan Ardo a yankin Janjala na karamar hukumar Kagarko a Kaduna cewa, sun kashe tare da binne matar shugaban kauyen, Abubakar Ardo da suka sace.
Hakazalika, sun bukaci iyalan nasa da su yi mata addu’ar rahama tunda ita kam sun shilla ta kiyama, inji rahoton Daily Trust.
Wakili Usman, wani dangin Ardo ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar a ranar Talata, inda yace tsagerun sun shaidawa ahalin haka ne a lokacin da suka bukaci a ba su gawarta.
A cewarsa, dangin sun roki ‘yan bindigan da su taimaka su ba da gawar matar, amma suka ji batu mara dadi daga bakin shugaban ‘yan ta’a’ddan cewa sun ma binne ta tuntuni a dajin da suke boye.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda lamarin ya faru
Madakin Janjala, Samaila Babangida ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace:
“Bana nan na tafi Jere sai aka kira ni cewa ‘yan bindigan sun kira sun ce tuni sun binne matar Ardo a maboyarsu. Abin da muka yi kawai shine yi mata sallah a nan.”
Ya kuma shaida cewa, da yawan mutanen Janjala, musamman mata da yara sun kaura daga yankin saboda yadda ‘yan ta’adda suka addabi kowa.
Sace matar da kuma hallaka ta bayan karban fansa
Idan baku manta ba, rahoto a baya ya bayyana yadda ‘yan bindigan suka kashe matar sarkin Fulanin mai suna Hulaira Abubakar Ardo bayan karban kudin fansa N2m daga mijin.
Kasancewar sun sace matan basaraken ne hudu gaba daya, sun sako uku a lokacin da suka karbi N2m, amma suka rike matar da suka kashen.
Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba game da lamarin mai daukar hankali.
Asali: Legit.ng