Tashin Hankali Yayin da Tsohuwa Ta Bankawa Danta, Matarsa da Jikokinta Wuta
- Wata mata ta hallaka danta, matarsa da kuma jikokinta a lokacin da ta banka musu wuta a jihar Ondo
- Rahoton da muka samo ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma yadda mutum uku suka rasu
- Ya zuwa yanzu, ba a samu labarin ainihin dalilin da yasa tsohuwar ta aikata wannan danyen aikin ba
Jihar Ondo - Wata mata mai shekaru 75 ta bankawa danta, surukarta da jikokinta biyu wuta a jihar Ondo da ke Kudu maso Yamma.
Ana zargin tsohuwar mai suna Iforiti Oloro ta wanke gidan da suke rayuwa ne da man fetur, inda take rayuwa tare da danta Victor Oloro da kuma ahalinsa.
Rahoton Daily Trust ta bayyana cewa, wannan lamarin ya faru ne a yankin Aponmu da ke kusa da birnin Akure na jihar.
Wata majiya da ta tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari a ranar Talata ta ce, an dauki wadanda suka konen zuwa asibitin tarayya da ke Owo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An ruwaito cewa, daga baya asibitin ya tabbatar da mutuwar dan nata, matarsa da kuma daya daga yaran nasu a hadarin.
A cewar majiyar:
“Dansu na fari ne kadai ya tsira amma yana cikin mawuyacin hali a yayin da nake magana daku.”
'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Wani rahoton jaridar Gazette na bayyana cewa, matar ta sha afkawa don sheke kanta a lokuta daban-daban.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Fanmilayo Odunlami Omisanya ta tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai, har yanzu rundunar na jiran cikakkun bayanai game da gaskiyar yadda lamarin ya faru daga ofishin ‘yan sanda na yankin.
Ta ce:
“Har yanzu ina jiran cikakkun bayanai game da lamarin daga DPO da ke kula da yankin. Don haka, ina bukatar ku kara bani karin lokaci don tattara bayanai.”
‘Yan bindiga sun rike mijin da ya kai kudin fansa don karbo matarsa
A wani labarin, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka kai farmaki tare da sace mata da ‘ya’yanta a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma.
Mijinta ya dauki kudi N2m don kaiwa ‘yan bindigan a matsayin kudin fansa, sai kawai suka rike shi tare da neman karin kudi.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da farmakin ‘yan bindiga a Najeriya, musannan cikin shekarun nan.
Asali: Legit.ng