'Yan Bindiga Sun Rike Wani Mutumin da Ya Kai N2m Na Fansar Matarsa Da ’Ya’yansa 3 da Aka Sace
- Rahoton da muke samu daga jihar Kaduna ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka rike wani mutumin da ya kai musu kudin fansa
- Wannan lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan kashe wata mata a yankin Janjala da ke karamar hukumar Kagarko
- Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman a cikin shekarun baya-bayan nan
Jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun rike wani mutumin da ya kawo kudin fansa don a sake matarsa, dansa da ‘ya’yansa mata biyu da aka sace a Anguwar Janruwa da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
An ruwaito cewa, makwanni biyu da suka gabata ‘yan bindiga sun farmaki Anguwar Janruwa a yankin Janjala, inda suka sace matar aure Hauwa Abubakar, danta Idris Abubakar da ‘ya’yanta mata Ummi da Sadiya.
Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, wani dangin wadanda aka sacen, Audu Bajeko ya ce, dan uwan nasa, Abubakar Ardo ya kwashi kudi N2m domin kai wa ‘yan bindiga a inda suke a ranar Lahadi, amma suka rike shi.
Miliyan 20 ‘yan bindigan ke nema
Ya bayyana cewa, bayan rike mutumin, sun nemi a biya kudin fansa N20m kafin su sako shi da dukkan iyalansa, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Da kusan karfe 5:30 na yamma ranar Lahadi, lokacin ne shugaban ‘yan bindigan ya kira don sanar dasu cewa sun rike mutumin da ya kawo N2M na fansa don a sake matarsa da ‘ya’yansa.
“Da aka tambaye shi meye yasa, dan bindigan ya ce adadin kudin da ya nema ba su mutumin ya kawo ba.”
Bajeko ya bayyana cewa, shugaban ‘yan bindigan ya ce ba zai saki dukkan ahalin ba har sai an cika N18m na fansan su.
Ya kara da cewa, a halin da ake ciki kowa a dangin ya shiga tashin hankali, inda yace N2m din ma da aka hada an sha fama matuka ainun.
Akwai matsalar ‘yan bindiga a Janjala, shugaban yanki ya koka
Madakin Janajal, Samaila Babangida, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, lamarin ‘yan bindiga na ci gaba da jefa al’umma cikin mummunan hadari da rudani.
A kalamansa:
“Kwana biyun da suka gabata, aka kashe uwar gidan Ardo Fulani bayan karban kudin fansa N2m daga ahalin, da safen nan kuma muka samu labarin mutumin da ya je karbo iyalansa shi ma an rike shi bayan ba da N2m.”
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su taimakawa al’ummar yankin ta hanyar taimaka musu da daukin yakar ‘yan bindigan da ke ta’addanci a yankin.
Ya zuwa yanzu, babu wani bayani daga hukumomin tsaro na ‘yan sanda soji har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A jihar Borno kuma, sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP da suka kai hari cibiyar tattara sakamakon zabe.
Asali: Legit.ng