Hukumomin Tsaro Na Cikin Shirin Ko-ta-kwana a Kaduna Yayin da Ake Fargabar barkewar Rikici Bayan Zabe

Hukumomin Tsaro Na Cikin Shirin Ko-ta-kwana a Kaduna Yayin da Ake Fargabar barkewar Rikici Bayan Zabe

  • Jami'an tsaro a jihar Kaduna na cikin shirin ko-ta-kwana kan yiwuwar barkewar rikicin siyasa a jihar
  • Gwamnatin Kaduna ta ce ta samu bayanan sirri na shirin da wasu ke yi don ta da zaune tsaye a jihar
  • Kwamishinan tsaron cikin gida na ya gargadi mazauna jihar da su guji karya doka da oda ko su fuskanci hukunci

Kaduna - Gwamnatin Kaduna ta bukaci mazauna jihar da su guji duk wani rikici domin hukumomin tsaro a jihar na cikin shirin ko-ta-kwana don dakile barazana ga doka da oda.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa an sanar da sakamakon zabe daga kananan hukumomi 19 cikin 23 a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris kafin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta dage shirin tattara sakamakon.

Ana sanya ran za a sanar da sauran sakamakon kananan hukumomi hudu da ya yi saura da zaran an dawo a yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Hana FitaDaga Safe Har Dare

Yadda jami'an tsaro ke shirin magance rikici a Kaduna
Jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Gwamnatin Kaduna ta samu bayanan sirri kan shirin ta da zaune tsaye da wasu ke yi

A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya saki a ranar Litinin, 20 ga watan Maris, ya ce gwamnatin jihar ta samu bayanan sirri kan shirin da wasu ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bayanan ya nuna shirin da wasu mutane da kungiyoyi na kokarin haddasa rikici a garin Kaduna da sauran manyan cibiyoyi a jihar.

Jaridar Vanguard ta nakalto Aruwan yana cewa:

"Hukumomin tsaro na bincike sosai cikin wadannan rahotannin. Za a dauki tsattsauran mataki kan duk mutum ko kungiyoyi da aka samu da hannu a cikin irin wadannan ayyuka.
"Yana da matukar muhimmanci mu jaddada cewa har yanzu an haramta zanga-zanga a unguwanni don hana yiwuwar karya doka da oda.
"Gwamnati na rokon jama'a da su kai rahoton kowani aiki da ka iya zama barazana ga zaman lafiya, doka da oda ta wadannan layukan wayan: 09034000060 08170189999.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

Zaben Gwamna: Gwamnatin Kano ta saka dokar hana fita

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita a fadin jihar bayan sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

An dauki wannan matakin ne don hana barkewar rikici da oda a jihar wacce dauki dumi sakamakon zaben gwamnan wanda aka yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng