Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Halaka Kasurgumin Dan Ta'adda a Jihar Zamfara
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka wani ƙasurgumin ɗan ta'adda a jihar Zamfara
- Sojojin sun halaka ɗan ta'addan ne mai suna Ummaru Nagona a yayin wata Arangama
- Ummaru Nagona ya fitini yankunan Gabashin Sokoto da hare-hare lokacin da yake raye
Jihar Zamfara- Dakarun sojojin Najeriya sun halaka wani ƙasurgumin ɗan ta'adda da ya addabi mutanen yankin Arewa maso Yamma.
Dakarun sojojin sun samu nasarar halaka Ummaru Nagona, wanda yayi ƙaurin suna wajen ta'addanci a yankunan jihohin Sokoto da Zamfara. Rahoton Daily Trust.
A lokacin da yake raye yana aikata ta'addancin sa, Ummaru Nagona yafi mayar da hankali akan yankunan Gabashin jihar Sokoto, musamman ƙauyukan Isa da sabon birni.
Mazaunan yankin dai sun sha matuƙar wahala a hannun ɗan ta'addan lokacon da yake raye. Ya kuma yi aiki tare da ƙungoyoyin ƴan ta'adda daban-daban.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake magana kan kisan ɗan ta'addan, tsohon wakilin jaridar Daily Trust wanda ya sha kawo rahotanni tsaro ya tabbatar da halaka ɗan ta'addan da sojoji suka yi a wani rubutu da yayi a shafin sa na Facebook.
A kalamansa:
"Yanzu nake samun tabbacin kisan babban ɗan bindiga, Ummaru Nagona a wata arangama da sojojin Najeriya a ranar Laraba da ta gabata."
"Motar atilare ta soja ce ta take shi akan mashin da yake kai tare da yaron da ya goyo shi akan hanyar su ta zuwa kai agaji sakamakon harin da sojojin suka kai a sansanin ƴan bindiga a yankin Kagara ta gabacin Shinkafi."
"Na haɗu da Ummaru Nagona a ziyara ta wurin Bello Turji a watan Disamba na shekarar 2021. Idan ka gan shi ba ka ce ɗan bindiga ba ne. Mugu bai da kama!"
Har ya zuwa wannan lokacin dai rundunar sojojin bata ce komai ba kisan da aka yiwa ƙasurgumin ɗan ta'addan.
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 60 da Ke Kokarin Farmakar Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe a Borno
A wani labarin na daban kuma, sojoji sun halaka ƴan ta'adda da dama a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun dai je farmakar cibiyar tattara sakamakon zaɓe ne.
Asali: Legit.ng