Kwankwaso Da Buba Galadima Sun Dira Ofishin INEC A Kano Yayin Da Ake Jiran Sakamako Zabe

Kwankwaso Da Buba Galadima Sun Dira Ofishin INEC A Kano Yayin Da Ake Jiran Sakamako Zabe

  • Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023 da jigon NNPP, Buha Galadima sun tafi dira cibiyar tattara sakamakon zaben Kano
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano sun tafi cibiyar tattara zaben ne a yayin da ake zaman jiran a sanar da sakamakon duk da cewa an kammala kawo kuri'u
  • Tunda farko jigon na NNPP ya bukaci magoya bayan jam'iyyar su raka kuri'arsu zuwa cibiyar tattara sakamakon zaben don gudun magudi

Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), da Injiniya Buba Galadima, jagoran jam'iyyar NNPP sun dira ofishin hukumar zabe mai zaman kanta INEC.

Mutanen biyu suna wajen ofishin na INEC a yayin da dubbanin magoya bayansu ke waje a tare da su suna jiran a sanar da sakamakon zaben gwamna da aka yi tun ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Kwankwaso
Kwankwaso Da Buba Galadima Sun Dira Ofishin INEC A Kano Yayin Da Ake Jiran Sakamako Zabe. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana tattara kuri'un zaben a nan kuma alkalluma daga kananan hukumomi 44 na jihar da aka sanar sun nuna jam'iyyar adawar ke kan gaba, rahoton Daily Trust.

Amma, baturen zabe, ya ce yana bukatar lokaci ya yi aiki kan fam din.

Hakan ya sa zargi tsakanin wakilan jam'iyya da magoya baya da ke cibiyar tattara sakamakon zaben, amma jami'an INEC sun tabbatar musu komai na tafiya dai-dai.

Masu zabe sun ki karbar tiransifa ta kudi a a jihar Neja

A wani rahoton, wasu cikin wadanda suka tafi kada kuri'arsu a karamar hukumar Tafa ta jihar Neja sun ki yarda da alkawarin tiransifa da aka musu daga wakilan jam'iyyu suka ce sun gwammace a ba su abinci kafin su yi zaben a ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

An kuma: Hukumar INEC ta ayyana zaben wani yankin Kano 'Inconclusive'

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wasu cikin masu zaben sun ce an musu irin wannan alkawarin na tiransifa a baya yayin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu amma ba a cika musu ba.

Wata cikin wadanda suka yi zaben da ta ce sunanta Angela, ta ce suna sane cewa abin da suka aikata laifi ne karkashin dokar kasa kuma amma dai hakan ne hanya guda da za su iya morar yan siyasan domin ba za su sake ganinsu ba sai wani zaben.

Jam'iyyar PDP ta ce za ta tafi kotu kan sakamakon zaben gwamnan Katsina

A wani rahoton, jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta ce ba ta amince da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar, tana mai cewa za ta tafi kotu.

Dr Mustapha Inuwa, direktan kwamitin yakin neman zaben Atiku/Lado ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da ya kira ranar Litinin a Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164