INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Ne Ya Lashe
Dauda Lawal, dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben gwamnan da aka yi a jihar Zamfara a makon nan, inda ya tumbuke gwamna mai ci, Bello Matawalle na APC.
Baturen zabe na INEC a Zamfara, Farfesa Kasimu Shehu ne ya bayyana cewa, Dauda ya samu kuri'u 377,726 inda gwamnan kuma ya samu kuri'u 311,976, Daily Trust ta ruwaito.
Idan baku manta ba, an samu cece-kuce da rikici a lokacin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar, lamarin da ya kai ga sace wasu jami'an INEC biyu.
Sakamakon zaben gwamna ya fara fitowa daga jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sakamakon zaben ya nuna cewa, Dauda Lawal ya lashe Zaben ne daga kananan hukumomi 10, inda Matawalle ya samu kuri'unsa mafi yawa daga kananan hukumomi biyu kacal.
PDP ta zargi APC da daukar dumi a Zamfara
A bangare guda, wani rahoton jaridar SaharaReporters na cewa, jam'iyyar PDP ta zargi ta APC da kokarin yiwa jami'an zabe barazana a wasu kananan hukumomin jihar.
A cewar PDP, dukkan sakamakon zaben da aka daura a kafar yanar gizo sun nuna PDP ce ya yiwa APC cin kaca.
Wannan zargi na PDP dai na fitowa ne daga wata sanarwar da aka yi a Gusau a ofishin hadimin dan takarar gwamnan jam'iyyar.
Ya bayyana cewa, alamu sun nuna gwamnatin jihar mai ci bata ji dadin yadda sakamakon zaben ke fitowa da nasarar PDP ba.
Za a ci gaba da tattara sakamakon zabe
Bayan dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Zamfara a daren jiya Lahadi 19 ga watan Maris, a yau ne za a ci gaba da kawo sakamakon daga kananan hukumomin jihar.
A jiya, an kawo sakamakon kananan hukumomi uku; Zurmi, Anka da Bukuyum, inda yau ake tsammanin kawo sauran 11 da suka rage cikin 14 na jihar.
Sauran kananan hukumomin da suka rage sune; Gusau, Tsafe, Bungudu, Maru, Bakura, Talata Mafara, Maradun, Gumi, Kaura-Namoda, Birnin Magaji da Shinkafi.
Sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara
1. Karamar hukumar Birnin-Magaji
APC - 9,643
PDP - 8,991
2. Karamar hukumar Maradun
APC - 24,855
PDP - 12,261
3. Karamar hukumar Maru
APC - 10,646
PDP - 22,036
4. Karamar hukumar Gusau
APC - 32,172
PDP - 64,710
5. Karamar hukumar Kaura-Namoda
APC: 26,472
PDP: 31,236
6. Karamar hukumar Shinkafi
APC: 13,408
PDP: 13, 435
7. Karamar hukumar Tsafe
APC - 25,805
PDP - 42,188
8. Karamar hukumar Bakura
APC - 41,063
PDP - 19,455
9. Karamar hukumar Talata-Mafara
APC - 41,280
PDP - 22,236
10. Karamar hukumar Bungudu
APC - 24,865
PDP- 47,464
11. Karamar hukumar Gummi
APC - 20,263
PDP - 27,929
12. Karamar hukumar Anka
APC - 10,156
PDP - 17,116
13. Karamar hukumar Bukuyum
APC - 10,321
PDP - 24,341
14. Karamar hukumar Zurmi
APC - 21,027
PDP - 24,328