‘Ku Zabi APC Ko Ku Zauna a Gida’: Bidiyon Yadda ‘Yan Daba Ke Yiwa Masu Kada Kuri’ Barazana a Legas
- An samu tsaiko yayin da wasu 'yan daba suka yiwa mutane barazana a wani yankin jihar Legas
- An ga bidiyo na yawo na yadda matasan ke cewa, ko dai mutane su zabi APC ko kuma su zauna a gida
- Ya zuwa yanzu da ana ci gaba da zabukan gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a fadin kasar nan
Jihar Legas - An ga wasu da ake zargin ‘yan daba ne a cikin wani bidiyo suna yiwa masu kada kuri’u barazana a jihar Legas, daya daga cikin jihohin APC da ake zaben gwamna da ‘yan majalisun jihohi.
A bidiyon da aka gani, an ga wasu ‘yan daba kusan takwas a kan titi suna yiwa jama’a gargadin ko dai su zabi jam’iyyar APC ko kuma su koma gida su zauna kawai.
A cewar daya daga cikinsu:
“Idan ba za su zabi APC ba, kada ku fito waje. Wannan ba irin na wancan lokacin bane.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsoron da ke ran APC a Legas
Peter Obi na jam’iyyar Labour ya lallasa zababben shugaban kasa, dan takarar APC Bola Ahmad Tinubu a Legas duk da ku shi dan asalin jihar ne.
Jam’iyyar APC ko nau’inta ne ke mulkar jihar Legas tun 1999, kuma Tinubu ya kasance gwamnan jihar na wa’adi har biyu.
An samu tsaiko da rikice-rikice a lokacin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An yiwa Inyamurai gargadi a Legas
An ruwaito yadda ake yiwa jama’ar Inyamurai gargadi da barazana a jihar ta Legas, musamman daga bakin shugaban hukumar kula da tashoshin mota, Musuliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluoma.
Da yake zantawa da magoya bayan jam’iyyar APC a wani taro, MC Oluoma ya gargadi Inyamurai kan cewa, idan ba za su zabi APC ba, to su zauna a gida.
Buhari na son Tinubu ya ci gaba daga inda ya tsaya
A wani labarin, kun ji yadda shugaba Buhari ya bayyana bukatar gwamnati mai zuwa ta ci gaba da yakar rashawa kamar yadda ya yi.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya saura masa kwanaki kadan ya tattara ya fice daga Aso Rock Villa da ke Abuja.
Ya zuwa yanzu, Tinubu ya yi alkawarin yin kadan daga abubuwan da Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng