Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Bauchi da Gombe a Arewacin Najeriya

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
6 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Salisu Ibrahim avatar
daga Salisu Ibrahim

Jama'a na ta fitowa a Gombe don kada kuri'u, suna tattaki

Rahotanni daga jihar Gombe sun nuna cewa, an samu jama'ar gari da yawa da suka fito domin kada kuri'unsu a zaben da ke gudana a yau Asabar.

Mazauna unguwannin Madaki, Sabon Layi a Bolarim Herwagana da Kumbiya-kumbiya sun fito domin zabe.

Hakazalika, an ga mutane da yawa na tattakin zuwa rumfunan zabe a wasu unguwannin jihar ta Gombe, rahoton Premium Times.

An ga jami'an tsaro sun isa wasu rumfunar zaben tun misalin karfe 6:55 na safe don tabbatar da tsaro a jijar.

Haka nan, masu kada kiri'u da yawa ne suka fito kada kuri'un a unguwanni daban-daban na jihar.

Salisu Ibrahim avatar
daga Salisu Ibrahim

Zabe a karamar hukumar Kaltungo ta jihar Gombe

An fara kada kuri'u a rumfa ta 022 a karanar hukumar Kaltunga ta jihar Gombe da ke Arewa maso gabas.

Sai dai, an ga turawan zaben na zaune a kasa suna aikinsu babu kujera ko teburin zama a yi aikin.

Salisu Ibrahim avatar
daga Salisu Ibrahim

Ana ci gaba da zabe cikin tsanaki a jihar Bauchi

Ya zuwa karfe 9:03 na safe, tuni an fara zabe a Kofar Yalawa da ke gundumar Sakwa a karamar hukumar Zaki ta jihar Bauchi.

Salisu Ibrahim avatar
daga Salisu Ibrahim

Jami'an zabe sun iso Kataugum, za a fara zabe

Jami'ai da turawan zabe sun iso gundumar Nasarawa B, rumda ta 041 da ke Katagum a jihar Bauchi.

Salisu Ibrahim avatar
daga Salisu Ibrahim

An fara kada kuri'u a Darazau, jihar Bauchi

Da misalin karfe 8:48 aka fara kada kuri'u a gundumar Wahu rumfa ta 001 da ke karamar hukumar Darazau a jihar Bauchi.

Salisu Ibrahim avatar
daga Salisu Ibrahim

Jami'an tsaro da turawa zabe sun iso rumfunar zabe a Makama Sarkin Barki ta Demsa a Bauchi

Da misalin karfe 7:29 ne ma'aikatan zabe da jami'an tsaro suka iso rumfar zabe ta 002 ta Makama Sarkin Barki dake karamar hukumar Demsa ta jihar Bauchi.