Ruwan Bama-Bama Soji Ya Halaka Kwamandojin Yan Ta'adda a Borno
- Rundunar sojoji ta samu babbar nasara a wani luguden sama da ƙasa da ta kaddamar kan mayakan ISWAP a Borno
- Zagazola Makama ya ce bayanai sun nuna akalla mayaƙan ISWAP 70 ne suka baƙunci lahira sakamakon harin sojin
- A 'yan watannin nan, Dakarun soji sun hana yan ta'adda sakat a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya
Borno - Aƙalla mayaƙan ISWAP 70 ciki har da manyan kwamandojinsu ne suka sheƙa barzahu sakamakon luguden wutan sojin Najeriya ta sama da ƙasa a jihar Borno.
Zagazola Makama, masani kuma mawallafin da ya maida hankali kan sha'anin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya tabbatar da nasarar sojojin a shafinsa na Tuwita.
Ya ce bayanan sirrin da ya samu sun nuna cewa rundunar sojin Operation Haɗin Kai, rundunar sashi na 3 ta sojojin gamayyar kasashe (MNJTF) da dakarun sashi na 4 na MNJTF ne suka kai samame ta sama da ƙasa kan 'yan ta'addan.
Bayanan sun ƙara da cewa a ranar Laraba, Dakarun sojin suka nazarci tare da tunkarar muhimman wuraren ɓoyon mayakan ISWAP da ke Kusuma, Jibularam, da Kwalaram kafin daga bisani su farmake su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Bayanan da suka biyo baya sun tabbatar da cewa cikin nasara luguden wutan ya halaka mayaƙa 70, ciki har da manyan kwamandoji, mayaƙan ƙafa, yan Hisbah duk na ƙungiyar ISWAP."
- Zagazola Makama.
Wata majiya ta shaida wa Makama cewa harin ya yi nasarar lalata kayan aikin 'yan ta'addan, kama daga Motoci, Mashina da muggan makamai.
Bugu da ƙari, majiyar ta bayyana cewa luguden wutan ya raba da yawan yan ta'addan da wuraren da suke ɓuya, inda ɗaruruwan mayakan suka tsere zuwa yankin Marte domin ceton rayuwarsu.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a 'yan makonnin nan, Sojin Najeriya sun matsa ƙaimi wajen kai samame wuraren ɓoyon 'yan ta'adda a shiyyar arewa maso gabas.
Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace Sama da 60
A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Halaka Basarake da Wasu 2, Sun Sace Mutane Sama da 60 a Jihar Neja
Wasu mahara da suka kwashe awanni suna aikata ɗanyen aiki a kananan hukumomi biyu a jihar Neja, sun kashe Basarake.
Asali: Legit.ng