Za a Sake Gudanar da Zabukan Sanata da Na ’Yan Majalisun Tarayya a Jihohi 15 Na Najeriya
Za a sake zaben ‘yan majalisun tarayya a gobe Asabar 18 ga watan Maris a mazabun sanata takwas da na ‘yan majalisun tarayya 33 a jihohi 15 na kasar nan.
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), maimaita zaben kujeru 41 na majalisar dokokin tarayyan za a yi shi ne tare da na gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha.
Ba a yi zaben sanata ba a mazabar Enugu East biyo bayan mutuwar dan takarar jam’iyyar Labour kwanaki kadan kafin zaben ranar 25 ga watan Maris, The Nation ta ruwaito.
Hakazalika, ba a yi zaben ba a mazabar Esan Central/Esan West/Igueben a jihar Edo saboda bacewar tambarin daya daga cikin jam’iyyun siyasan kasar nan.
Yadda ta kaya a jihar Sokoto
A jihar Sokoto, an soke zaben mazabun sanata uku da na ‘yan majalisun tarayya 11 saboda ballewar rikici, don haka hukumar zaben ta ce za a sake yin zaben a ranar Asabar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar rahotanni, za a sake zaben na mazabu daban-daban na jihar ta Sokoto da wasu jihohi 14 a Najeriya.
A bangare guda, duk da an ayyana Alhassan Ado Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar tarayya a mazabar Doguwa/Tudun Wada, INEC ta soke nasarar tasa, inda tace an tursasa jami’in zabe ya ayyana shi, Punch ta ruwaito.
Mazabun da za a yi zaben sanata gobe Asabar
- Enugu East (Enugu)
- Kebbi North (Kebbi)
- Plateau Central (Plateau)
- Yobe South (Yobe)
- Zamfara Central (Zamfara)
- Sokoto East, North da South (Sokoto)
Mazabun da za a sake zaben ‘yan majalisun tarayya
- Akwa Ibom - Abak/Etim Ekpo/Ika and Ikono/Ini
- Edo - Esan Central/Esan West/Igueben and Orhionmwon/Uhunmwode
- Imo - Ikeduru/Mbaitoli and Isu/Njaba/Nkwere/Nwangele
- Kano - Doguwa/Tudun Wada and Fagge
- Kebbi - Arewa/Dandi and Koko/Besse/Maiyoma
- Oyo - Ibadan Northeast/Ibadan Southeast and Oluyole
- Rivers - Gokana/Khana and Port Harcourt II
- Zamfara - Gummi/Bukkuyum and Gusau/Tsafe
- Taraba - Takum/Donga/Ussa
- Kogi - Bassa/Dekina
- Jigawa - Gumel/Maigatari/Sule Tankarkar/Gagarawa
- Ebonyi - Ezza North/Ishielu
- Bayelsa - Southern Ijaw
- Anambra – Igbaru
Idan baku manta ba, a jihohi 28 ne za a yi zaben gwamnoni a Najeriya, kasancewar wasu jihohi tara suna yin zabensu ne a lokaci na daban.
Wannan ya faru sakamakon wasu matsalolin da ke alaka da doka da kuma rikicin kotu na bayan zabuka.
Asali: Legit.ng