Bidiyon Yadda Matashi Ya Tsinci Yarinya a Bakin Titi Ya Taimake Ta Ya Jika Zukatan Jama’a

Bidiyon Yadda Matashi Ya Tsinci Yarinya a Bakin Titi Ya Taimake Ta Ya Jika Zukatan Jama’a

  • Wani dan Najeriya ya yada wani bidiyo mai taba zuciya na yadda ya tsinci wata yarinya a bakin titi sannan ya taimake ta
  • A bidiyon, an ga karamar yarinyar na zaune a kasa a bakin hanya sai kuma ga matashin ya zo domin ya taimake ta a yanayin da take ciki
  • Matashin ya dauke ta, inda ya sauya mata tufafi, ya ba ta abinci da abin sha, ya yi mata gatan da ya bata yi tsammani ba

Wani bidiyon da wani matashi ya yadu a kafar sada zumunta ya dauki hankalin jama’a, ya kuma taba zukatan mutane da yawa.

Bidiyon da matashin ya yada ya nuna wata yarinya mai launin bakin fata zaune ita kadai, da alamun tana cikin kunci, babu kulawa.

An ga yarinyar a zaune a kasa a kan dandamali ga kuma lokacin da matashin ya tsaya domin ya taimake ta.

Kara karanta wannan

"Na Taki Sa'ar NYSC": Budurwa Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

Ya dauke ta ya kaita inuwa, ya nemo mata abinci da ruwa da kayan makulashe kana ya sauya mata tufafi.

Yadda matashi ya tsinci yarinya a titi
Hotunan lokacin da ya tsinci yarinyar | Hoto: @feedmissionuganda0
Source: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mutumin, ya samu ta ne kan titi sai kawai ya yanke shawarin daukarta don yi mata gata.

Bidiyon ya jika zukatan jama'a

Bidiyon ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, inda mutane da yawa ke yaba masa da kuma yin ta’ajibin abin da ya aikata wa yarinyar na kirki.

Ga dai abin da ya rubuta lokacin da ya yada bidiyon:

“Na tsince ta ne a kan titi, na taimake ta da kadan din da nake dashi.”

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@Kia:

"Ina son taimakawa ta hanyar gidan marayu. Ba da abinci na raga daya yana da kyau, amma ya gobe za ta kasance da kuma tsaronta?”

@sharoanda davis:

"Allah ya albarkaci wannan yarinyar da tsaftataccen wuri don ta rayu.”

@MelissaClyde:

"Ba zan iya barinta ba, zan tafi da ita da nine.”

Kara karanta wannan

An Kama Bokan Da Ke Yi Wa Mutane Alkawarin 'Azirta' Su Ba Tare Da Amfani Da Sassan Jikin Dan Adam Ba A Edo

@Egyptian Blu:

"Ina uwar ko kuma uban? Ka same su? Ina fatan ba barinta ka yi ba.”

@DreaToomuch:

"Har na mutu zan tuna ki.”

@lori:

"Ka mai da ita ‘yarka, kada ka barta ita kadai.”

@Mainecarter511:

"Allah ya yi maka albarka da wannan taimako.”

@lilah:

"Kana da kirki sosai, Allah ya yi maka albarka.”

@Antoinette Thacke475:

"Ina ma a ce zan same ta. Allah ya maka albarka da ita ma.”

A wani labarin, kun ji yadda wani matashi ya kama sana'ar fawa duk da kuwa yana dan kabilar Inyamurai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng