Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na Bana Ya Ba Mutane da Yawa Mamaki, Inji Garba Shehu

Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na Bana Ya Ba Mutane da Yawa Mamaki, Inji Garba Shehu

  • Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wasu ‘yan Najeriya sun kadu da sakamakon zaben bana
  • Ya bayyana cewa, duk da an samu tsaiko a zaben bana, amma a hakan shi ne zaben dama-dama da aka yi a tarihin Najeriya
  • Jam’iyyun adawa na ci gaba da bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaben shugaban kasan da aka yi

FCT, Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasan Najeriya, Malam Garba Shehu ya yi magana bayan da aka ayyana Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

A cewarsa, sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi ya girgiza da yawan ‘yan Najeriya kuma ya basu mamaki.

Garba Shehu ya bayyana wannan bayanin ne a ranar Alhamis 16 ga watan Maris da sanyin safiya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hangen nesa: Babban malami ya roki Buhari ya kori babban jami'in INEC saboda matsala 1

Garba Shehu ya yi martani bayan Tinubu ya lashe zabe
Garba Shehu da hoton ba Tinubu shaidar lashe zabe | Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

An samu matsala a zaben bana, amma shi ne dama-dama a tarihin Najeriya, inji Shehu

A cewarsa, duk da matsalolin da aka samu wajen aiwatar da zaben na shugaban kasa, zaben ne mafi kyau da aka yi a tarihin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa ta daban da Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin, ya ce gwamnatin Buhari ta kafa tubalin sahihin zabe a Najeriya.

Sai dai, ya ce ya rage wa hukumar zabe ta INEC da ta san yadda za ta bi ka’idojin da gwamnatin ta kawo don gudanar da zaben cikin tsanaki.

El-Rufai ya taya Tinubu murnar lashe zabe

A bangare guda, gwamnan jihar Kaduna ya taya Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa, inda yace tabbas dan siyasan ya cancanta ya gaji Buhari.

A cewar El-Rufai, Tinubu zai samar da duk abubuwan da ake bukata don ciyar da kasar gaba ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Mukarrabin Jonathan Ya Fadi Yaudarar da Tinubu ya yi Amfani da Ita Wajen Doke Atiku

Hakazalika, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi farin ciki da sakamakon zaben, inda yace gwamnatin Tinubu za ta samar musu abubuwan ci gaba masu yawa.

Obi da Atiku da Atiku sun tafi kotu

Sai dai, a bangaren ‘yan jam’iyyun adawa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour sun ce ba su amince da sakamakon zaben shugaban kasan ba.

A fahimtarsu, an yi murdiya a wurare da yawa, inda suka ce sam ba Tinubu ne ya kamata INEC ta sanar ya ci zabe ba.

Hakazalika, sun ce za su tafi kotu don tabbatar da an kwata musu hakkokinsu daidai da tanadin dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.