Oluwo Na Iwo Da Matarsa Yar Kano Sun Yi Haihuwar Fari Tare
- Abun farin ciki ya samu Oluwo na Iwo, Oba Adewale Akanbi, yayin da matarsa Gimbiya Firdaus ta samu 'karuwa
- Basaraken kasar Yarbawa mai daraja ta daya ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya don sanar da labarin ga mabiyansa
- Mutane da dama a soshiyal midiya sun taya basaraken da ahlinsa murnar wannan ni'ima da Allah ya yi masu
Babban basaraken kasar Yarbawa Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi, Oluwo na Iwo da kyakkyawar matarsa Firdausi sun yi haihuwar fari tare.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, Oluwo ya nuna godiyarsa ga Allah madaukakin sarki yayin da sanarwa mabiyansa da kyakkyawan labarin mai dadi.
Da yake wallafa hadadden hoton mai jegon, basaraken ya rubuta:
“Olodumare Oseun!! Ina godiya ga Allah madaukakin sarki da ya albarkaceni da kyakkyawar diya ta kyakkyawar sarauniyata....hip hip hip hurray. Allah ya albarkace ni."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kalli wallafar tasa a kasa:
Jama'a sun taya basaraken murna
bukkyojomu:
"Idan jinjirin nan na son zama sarki a gaba ina fatan ku yarbawa ba za su ce bahaushe bane."
lukamwanret:
"Ina taya ku murna."
rosythrone:
"Ina tayata murna. Abun farin ciki zai same mu dukka, abun nan da muke son Allah ya yi mana, zai zo ya wuce."
chef_ivyjones1:
"Ina taya ku murna! Allah ya karo albarka."
adornedbycheedah:
"Yaran da baka kula da su. kimanin mata biyar sun rabu da kai amma baka kula da yaran da suka haifa maka."
blackdepressionforum:
"Ina ganin wannan ne dansa na 10. Ina yiwa uwa da dan addu'an lafiya mai inganci."
grade_1_okrika_bag_shoes:
"Ina taya ma'auratan murna."
issa_nikola:
"Ku tuna cewa wata matashiya daga kasar Kanada ta haifa masa da da sannan ya mayar da ita ba bakin komai ba."
Magidanci ya yi wuff da kyakkyawar budurwa danya shakaf, bidiyon ya haddasa cece-kuce
A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a a soshiyal midiya sun yamutsa gashin baki bayan cin karo da hoto da bidiyon wani mutum da ya auri matashiyar budurwa mai jini a jika.
Abun da ya kawo cece-kuce a auren nasu shine duba ga yanayin mutumin wanda suka tabbatar da lallai akwai tazarar shekaru masu yawan gaske a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng