Farashin Gangar Danyen Mai Ya Fadi Zuwa $72, Karon Farko Tun Disamban 2021

Farashin Gangar Danyen Mai Ya Fadi Zuwa $72, Karon Farko Tun Disamban 2021

  • Farashin danyen man fetur ya fadi a kasuwar duniya, karo na farko kenan tun bayan shekarar 2021 ta bayan Korona
  • Wannan lamari ya shafi Najeriya kai tsaye, inda masani ya bayyana yadda hakan zai shafi tattalin arzikin kasar da ke Afrika
  • Najeriya ta dogara ne da mai a matsayin daya daga cikin hanyoyin samun kudin shiga, duk da ma akwai rikce-rikice a kai

Farashin mai ya fadi a ranar Laraba 15 ga watan maris zuwa $72 kan kowaccce a ganga a kasuwar duniya, karon farko kenan a kusan shekara guda.

Danyen man ya fadi a kasuwar duniya ne da kaso 5% zuwa $72.39 a kan kowacce, a karon farko kenan tun watan Disamban shekarar 2021.

Man Amurka na US West Texas ya kadi da kashi 5% shi ma, inda ya sauka zuwa $67.06 kan kowacce ganga, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Farashin Man Fetur Zai Lula, Gwamnatin Tarayya Tana Shirin Barin Tinubu da Jan Aiki

Gangar danyen mai ta koma $72 a duniya
Yadda farashin danyen mai ya fadi a duniya | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Meye ya faru mai ya sauka kasa?

A cewar rahoton Reuters, farashin kayayyaki ya sauka kasa yayin da ake ci gaba da damuwa da kamfanin Credit Suisse ya girgiza kasuwannin duniya da kuma tsammanin farfadowar bukatar mai ta kasar China.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hannun jarin Credit Suisse ya fadi da 30% a ranar Laraba bayan da bankin kasar Saudiyya na SNB, wanda yake babban mai hannun jari a Credit Suisse ya ce ya zare hannunsa ga tallafawa kamfanin.

Da yake magana game da fadurwar, Dennis Kissler babban mataimakin shugaban fannin cinikayya na BOK Financial ya ce, lamurra na ci gaba da tabarbarewa saboda hauhawar kudin ruwa da kuma rashin tabbas na tattalin arziki.

Farashin danyen mai da yadda sauyin ya shafi Najeriya

Farashin danyen man a halin yanzu bai kai $75 a kasafin kudin Najeriya na wannan shekarar ta 2023 ba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 Bayan Rasa Rayyuka 17, Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari

A 2020, lokacin da lamari irin wannan ya faru, Zainab Ahmed, ministan kudi a Najeriya ta ce gwamnatin kasar za ta rage iyakar kudin man zuwa $57.

Idan har za a yi duba ga maganar Zainab, gwamnati za ta yi waiwaye tare da sake komawa kan farashin farko na iyakar da ta sanya don ya zama daidai da tafiyar kasuwar duniya.

Bolade Agboola, wani fitaccen masanin fannin man fetur da gas a Meristem Securities Limited ya shaida cewa, wannan lamari zai zamewa Najeriya alheri, domin za ta samu kudin shiga da za a iya kashewa ga kasafin kudin shekarar.

A wani rahotonmu na baya, kunji yadda aka hango yiwuwar lulawar farashin man fetur na PMS a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.