Gwamna El-Rufai Ya Ware Makudan Kudade Domin Biyan Hakkokin 'Yan Fansho Da Gratuti
- Ana dab da zaɓen gwamna a Najeriya, gwamnatin jihar Kaduna ta sako kuɗaɗe domin a biya ma'aikata
- Gwamnatin jihar ta dai fitar da naira miliyan ɗari tara da ashirin (N920m) domin biyan haƙƙoƙin ƴan fansho
- Ƙuɗaɗen da gwamnatin ta fitar za a yi amfani da su wajen biyan haƙƙoƙin ƴan fanso, ma'aikatan da suka yi ritaya da kuma waɗanda suka rasu
Jihar Kaduna- Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da naira miliyan ɗari tara da ashirin (N920m) domin biyan bashin haƙƙoƙin ƴan fansho da gratuti na ma'aikatan jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar hukumar fansho ta jihar Kaduna, Farfesa Salamatu Isah, ta fitar a ranar Laraba a Kaduna. Rahoton Jaridar The Guardian ya tabbatar da hakan.
Tace kuɗin sun shafi rukuni 54 na ma'aikatan jiha dana ƙananan da suka yo ritaya da waɗanda suka rasa ran su. Rahoton The Cable
Ta kuma cigaba da bayyana cewa za a biya kuɗin ne da tsohon tsarin ”Defined Benefit Scheme (DBS)”.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sakatariyar ta kuma ƙara bayanin cewa ƴan fanshon na gwamnatin jihar da ma'aikata da suka yi ritaya zasu samu naira miliyan ɗari huɗu (N400m), yayin takwarorin su na ƙananan hukumomi za su samu naira miliyan ɗari biyar da ashirin (N520m).
Farfesa Salamatu Isah ta cigada da bayanin cewa biyan kuɗin wanda yake a ƙarƙashin shirin karo-karo na fansho wato 'Contributory Pension Scheme (CPS), zai biyo ne ta hannun Pension Funds Administrators (PFAs)
Jihar Kaduna Tayi Rashi, Babban Na'ibin Limamin Masallacin Sultan Bello Ya Rasu
A wani labarin na daban kuma, Allah ya yiwa na'ibin limamin masallacin sultan Bello dake Kaduna rasuwa.
Babban na'ibin limamin masallacin, Mallam Ibrahim Isah, ya rasu ne da safiyr ranar Laraba, 15 ga watan Maris 2023, a wani asibiti a cikin birnin Kaduna.
Rashin babban na'ibin limamin tabbas babban rashi ne ga al'ummar musulmai da mutanen jihar Kaduna. Mallam Ibrahim Isah, ya rigamu gidan gaskiya me bayan yayi fama da rashin lafiya, wanda har ya kai shi kwanciya a asibiti.
Asali: Legit.ng