'Yan Sanda Sun Halaka Dan Ta'adda Sun Kwato Makamai a Jihar Kaduna
- Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ta samu nasarar halaka wani ɗan ta'adda har lahira a jihar
- Rundunar ƴan sandan ta samu wannan nasarar ne bayan tayi fito na fito da ƴan ta'addan waɗanda suka tare wata hanya a jihar
- Jami'an ƴan sandan sun kuma samu nasarar kwato makamai a hannun ƴan ta'ddan yayin da wasu kuma suka samu munanan raunika
Jihar Kaduna- Jami'an tsaro sun yi bata kashi da ƴan ta'adda a jihar Kaduna inda suka samu nasarar halaka ɗaya daga cikin su, yayin da sauran suka arce da munanan raunika.
Rundunar ƴan sandan jihar ta Kaduna ta halaka ɗan ta'addan ne a ranar Talata, sannan ta kwato bindiga ƙirar AK-47, ɗauke da harsasai a cikin ta. Rahoton Channels Tv
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, shine ya bayyana wanann nasarar da jami'an rundunar suka samu cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Kisan Kai: Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Majalisar Tarayya Na Birni a Arewa Ruwa a Jallo, Sun Sa Lada N1m
A cewar kakakin, jami'an ƴan sandan rundunar waɗanda ke a ƙarƙashin Operation Whirl Punch (OPSWP), sun yi aiki ne sahihan bayanan sirri da suka samu cewa ƴan ta'adda sun tare hanyar titin Galadimawa-Tumburku, a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa jami'an ƴan sandan a ƙarƙashin jagorancin DPO na Kidandan sun hanzarta zuwa wajen, inda suka yi bata kashi da ƴan bindigan, sannan suka watsa shirin su na kai farmaki a hanyar.
Bayan sun ji ɓarin wuta ta ko ina, ƴan bindigan sun arce zuwa cikin dajin dake kusa da wajen ɗauke da munanan raunika. Rahoton The Guardian
Yan Sanda Sun Kama Yan Fashi Da Makami Sanye Da Kayan Sojoji
A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun samu nasarar cafke wasu miyagun ƴan fashi da makami sanye da kayan sojoji.
Ɓata garin da ake zargi da laifin na fashi da makami sun shiga hannu ne bayan sun kutsa kai cikin gidan wata baiwar Allah wacce bata san hawa ba, ba ta san sauka ba.
Waɗanda ake zargi da aikata laifin na fashi da makami sun kutsa cikin gidan matas ne da tsakar dare lokacin da sawu ya ɗauke.
Asali: Legit.ng