Yan Sanda Sun Kama Yan Fashi Da Makami Sanye Da Kayan Sojoji
- Yan sanda sun cika hannu da wasu mutane da ake zargin masu fashi da makami ne a jihar Edo
- Maharan sanye da kayan sojoji sun farmaki wata mata sannan suka raba ta da dukiya da kadarorinta
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, ya ce sun yi nasarar kwato wasu kayayyaki daga wajen barayin
Edo - Rundunar yan sandan jihar Edo ta kama wasu da ake zargin masu fashi da makami ne su hudu bayan sun farmaki gidan wata mata a garin Benin, babban birnin jihar Edo.
Barayin sun shiga gidan matar ne ta rufin gidan da misalin karfe 2:00 na tsakar daren Talata, 14 ga watan Fabrairu, Channels TV ta rahoto.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Chidi Nwabuse, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wata tattaunawa a ranar Talata, 14 ga watan Maris a garin Benin.
Yadda Yan Bindiga Suka Ki Sakin Ma'aurata Da Diyarsu Bayan Karbar N2m Kudin Fansa, Sun Sake Gabatar Da Wata Bukatar
Yadda mahara suka farmaki gidan wata mata a Benin, yan sanda
Ya ce wadanda ake zargin sun farmaki gidan matar sannan suka yi mata fashin kudade da kayayyaki masu muhimmanci a yankin Tenboga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin yan sandan ya ce wadanda aka kaman sun hada da Iyabo Victor, mai shekaru 35; Osas Aganmwonyi, mai shekaru 28; Nosa Owie, mai shekaru 24; da kuma Idi Etukudo.
A cewar Nwabuse, an kama wadanda ake zargin ne bayan rahoton da suka samu daga wacce aka yi wa fashin a gidanta.
Karkashin jagorancin Victor, wacce ake zargin sanye da kayan sojoji da bindigogi sun fasa gidan matar da ke garin Teboga sannan suka yi awon gaba da wayoyi da sarkokinta.
Kayayyakin da aka kwato a hannunsu
An tattaro cewa wadanda ake zargin sun tura N447,000 ta karfin tuwo daga asusun matar bayan sun karbi lambobinta na sirri.
Bayan sun tura kudin, Nwabuzor ya kara da cewar wadanda ske zargin sun sauya kudin zuwa kudaden waje sannan suka raba a tsakaninsu kafin a kama su, rahoton Nigerian Tribune.
Ya kara da cewar kayayyakin da aka kwato daga wajensu sun hada da wayar iPhone 13 da ya kai N500,000, iPhone 6, da ya kai N48,000 da sarkoki da ya kai N850,000.
Bayan sun karbi kudin fansa, yan bindiga sun ki sakin wasu iyali a Kaduna
A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindiga sun ki sakin wasu iyali da suka sace a yankin Janjala da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan 2 daga danginsu.
Asali: Legit.ng