Gwamna Matawalle Ya Yabawa CBN Kan Amincewa A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi
- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yayi maraba da umurnin babban bankin Najeriya kan tsaffin kuɗi
- Gwamnan ya bayyana umurnin na CBN kan a cigaba da amfani da tsaffin kuɗi a matsayin wata babbar nasara ga ƴan Najeriya
- Gwamna Matawalle yayi roƙo ga babban bankin Najeriya kan ya tabbatar kuɗaɗen sun wadatu domin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya ke ciki
Jihar Zamfara- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa umurnin da babban bankin Najeriya (CBN) yabi kan halaccin tsaffin kuɗi, nasara ce ga ƴan Najeriya.
Gwamnan yace yanzu al'umma sai su sanya ran su a inuwa domin ana tsammanin kuɗi za su wadatu a dalilin wannan umurnin na CBN. Rahoton The Cable
Babban Najeriya a ranar Litinin ya buƙaci bankuna da su riƙa bayar da tsaffin kuɗi sannan su karɓi tsaffin kuɗin na hannun mutane har zuwa 31 ga watan Disamba, kamar yadda kotun ƙoli tayi umurni. Rahoton Channels Tv
A wata sanarwa da Zailani Bappa, mai bayar da shawara na musamman kan watsa labarai ga Matawalle, ya fitar, gwamnan yace ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar kan sauya fasalin takaedun kuɗi, domin amfanin masu ƙananan sana'o'i ne da ƴan Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Waɗanda suka zarge mu zuwa kotu saboda zaɓen shugaban ƙasa duk da kukan da ƴan Najeriya ke yi kan sabon tsarin, yanzu sun ji kunya domin ba muyi ƙasa a guiwa ba har sai da muka samu nasarar buƙatar mu na ganin kawo ƙarshen sa."
“Hakan ya faru ne bayan mun daɗe da lashe zaɓen shugaban ƙasa."
“Dukkanin ƴan Najeriya yanzu hankulan su za su kwanta dangane da lamarin, sannan muna buƙatar kuɗaɗe su wadatu domin rage raɗaɗin da muke ciki."
"Yayin da kuma waɗanda ba su samu damar sauya tsaffin takardun kuɗaɗen su ba da sababbin waɗanda basu wadata ba, ba za suyi asarar kuɗin da suka tara gumi wajen neman su ba."
Gidan Man Gwamnan Ogun Ya Ki Karbar Tsoffin Naira Duk da Barazanar da Yake Yiwa ’Yan Kasuwa
A wani labarin na daban kuma, gidan man gwamna mai barazana ga ƴan kasuwa kan tsaffin kuɗi, ya ƙi karɓar tsaffin kuɗin a hannun mutane.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya dai yi barazanar kama duk wanda ya ƙi karɓar tsaffin kuɗin.
Asali: Legit.ng