CBN Ya Ba Da Umarnin A Ci Gaba da Amfani da Tsoffin N500 da N1000

CBN Ya Ba Da Umarnin A Ci Gaba da Amfani da Tsoffin N500 da N1000

  • Bayan sama da kwanaki 10, CBN ya yi biyayya ga hukuncin Kotun Koli wanda ta yanke ranar 3 ga watan Maris, 2023
  • CBN ya ce tsohon N500 da N1000 zasu ci gaba da yawo hannun yan Najeriya suna amfani da su har zuwa 31 ga watan Fabrairu
  • Babban bankin ya umarci bankunan kasuwanci su fara baiwa mutane tsohon naira kuma idan an kawo masu ajiya su karba

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya amince tsoffin N500 da N1000 su ci gaba da yawo a hannun yan Najeriya.

CBN ya tabbatar da haka ne a wata sanarwa da ya fitar ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na babban bankin, Isa Abdulmumin, ranar Litinin da daddare.

Tsoffin naira.
CBN Ya Ba Da Umarnin A Ci Gaba da Amfani da Tsoffin N500 da N1000 Hoto: CBN
Asali: UGC

A sanarwan da CBN ya wallafa a shafin Tuwita, ya umarci bankunn kaauwanci su fara baiwa mutane tsohom kuɗi kuma idan wasu sun kaso masu su karba.

Kara karanta wannan

Abokin Gamin Atiku Ya Roki 'Yan Najeriya, Ya Maida Martani Kan Ci Gaba da Amfani da Tsoffin N500 da N1000

Sanarwan ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Domin biyaayya ga umarni Kotu kamar yadda aka saba da kuma kara dankon bin doka da oda wanda halayya ce ta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari,"
"Babban Banki lamba ɗaya a Najeriya (CBN) yana mai umartan bankunan kasuwanci da ke da lasisin aiki a faɗin kasar nan su bi hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke ranar 3 ga watan Maris."
"Bisa haka, CBN ya gana da kwamitin bankuna kuma ya ba da umarnin cewa tsoffin N500 da N1000 zasu ci gaba da zama masu amfani tare da sabbin naira har zuwa 31 ga watan Disamba."

Tun da farko, gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, Chukwuma Charles, ya sanar da cewa CBN ya bi umarnin Kotun ƙoli.

Soludo ya yi bayanin cewa Telar bankuna ce zata riƙa haɗa lambobin ajiyar kuɗi maimakon Fotal ɗin CBN kuma babu karshen adadin da kowane mutum ko kamfani zai kai banki.

Kara karanta wannan

Gwamna APC Ya Faɗi Muhimmiyar Maganar da Ya Yi da Gwamnan CBN Kan Sauya Naira

Gwamnan ya ce Emefiele ne ya ba da wannan umarnin ne a wurin taron kwamitin bankuna wanda ya gudana ranar Asabar 12 ga watan Maris, 2023.

Buhari Ga Emefiele da Malami: Ku Bi Umarnin Kotun Koli Kan Tsohon Naira

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa gwamnan CBN da Malami umarni kan tsoffin N500 da N1000

A wata sanarwa da Mallam Garba Shehu ya fitar, ya ce babu dalilin da CBN zai fake da jiran umarnin shugaba Buhari kafin bin umarnin Kotun Koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262