Masu Yi Mani Fatan Mutuwa Za Su Mutu Kafin Ni, Tsohon Gwamna Orji
- Cif Theodore Orji ya magantu a kan jita-jitan da wasu ke yadawa game da shi cewa ya mutu
- Toshon gwamnan jihar Abia ya ce yana nan da ransa bai mutu ba kuma yana cikin koshin lafiya
- Orji ya ce duk masu yi masa fatan mutuwa sai sun mutu sun bar shi koda kuwa sun fi sa yaranta
Tsohon gwamnan jihar Abia, Cif Theodore Orji, ya yi watsi da jita-jitan da ke yawo cewa Allah ya yi masa rasuwa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa labarai sun yadu a jihar daga wasu majiyoyi da ba a tabbatar ba cewa tsohon gwamnan wanda aka fi sani da Ochendo ya mutu.
Rahotanni sun kawo cewa Orji wanda shine sanata mai wakiltan Abia ta tsakiya ya mutu a wani asibitin kwararru da ke Kaduna bayan ya je ganin likita kasancewar takardunsa na fita waje na a hedkwatar EFCC.
Sai dai kuma, a cikin wani bidiyo mai tsawon minti uku da ya saki wanda tuni ya yadu a soshiyal midiya, Ochendo ya karyata rade-radin mutuwarsa, rahoton Naija News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk masu yi mun fatan mutuwa sai sun mutu kafin ni, Orji
Ya ce duk masu yi masa fatan mutuwa sai sun mutu kafin shi.
Orji ya bayyana a bidiyon:
"Shakka babu, ina nan a raye. Ba ku ganina? Ba mutum bane yake magana?
"Rade-radin mutuwata baya nufin komai a gareni. Na sama da jita-jita; na saba da manyan jiga-jita. Don haka baya nufin komai a gareni.
"Ku da kuke abokaina ne kuka damu kuma kun zo tabbatarwa kuma kun ga gaskiya; cewa ina nan da raina. Ina nan daram dam.
"Jita-jita ne mai matugar muni. Wannan ba shine karo na farko da hakan ke faruwa a Abia ba.
"Mutane na shiga dakunansu, su kitsa labari sannan su fitar da shi kuma wadanda ke da saurin yarda sai su amshi tayin. Soshiyal midiya a bude take ga kowa kuma sai abokaina na kirki su fara dari-dari.
"Bana cikin damuwa ko kadan. Kuna da damar isa gareni kuma ga ni nan. Na kasance a Umuahia.
"Ba don dage zabe ba, da ina a rumfar zabena ina kada kuri'a."
Da aka tambaye shi game da fatan da yake yi wa masu masa fatan mutuwa sai ya ce:
"Ba a zubarwa a kwashe daidai. Idan ka yi mun fatan alkhairi, Allah zai maka fatan alkhairi.
"Idan ka yi mun mugun fata, mugun nufi zai bi ka. Shine abun da zai faru ga mutanen da ke yada jita-jitan cewa na mutu.
"Mutuwa na jiransu ko bajima ko badade. Za su mutu kafin ni. Koda kuwa sun fi ni yaranta, za su mutu kuma ni zan kasance daram dam."
A wani labari na daban, mun ji cewa watanni 14 bayan mutuwar tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, har yanzu ba a binne gawar Sanata Joseph Wayas ba.
Asali: Legit.ng