Dalla-Dallar Yadda CBN Ya Rabawa Duka Bankuna Sababbin N200, N500 da N1000 a Kwana 40

Dalla-Dallar Yadda CBN Ya Rabawa Duka Bankuna Sababbin N200, N500 da N1000 a Kwana 40

  • Mafi yawan sababbin kudin da CBN ya buga sun shiga bankunan Access Bank da ke Najeriya ne
  • Zenith Bank da First Bank da ke da yawan abokan mu’amala sun samu N28.441bn da N27.107bn
  • Legas ce a gaba idan ana maganar garuruwan da aka fi aikawa sababbin kudin, Enugu na baya

Abuja - Wani kebantaccen rahoto da aka fitar a WesternPost ya nuna abin da aka ba kowane bankin kasuwa na sababbin kudin da aka buga a Najeriya.

A Oktoban bara ne aka buga sababbin ‘Yan N200, N500 and N1000, amma kudin ba su fara yawo ba sai karshen Disamba, kuma har yanzu ba su yalwata ba.

Ganin wahalar da ake sha wajen hada-hadar ya jawo wasu Jihohi su ka kai kara a kotun koli, kuma a karshe aka ba su gaskiya a kan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Nufin Allah: Yadda Dangote da Abdul Samad suka ci ribar N300bn cikin sati daya

Jaridar ta samu ganin wata takarda da tayi kasafin abin da kowane banki ya samu daga N50bn da CBN ya raba daga karshen watan Junairu zuwa yau.

Wani banki aka fi sabon kudi?

Access Bank ya fi kowa samun kaso mai yawa a kudin, ya tashi da N33.484bn, sai Zenith Bank suka samu N28.441bn, sai aka ba First Bank N27.107bn.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bankunan UBA, GTCO da kuma FCMB sun tashi da N25.502bn, N19.594bn sai N16.01bn.

Bankuna
Kudin da aka ba bankuna Hoto:@mrabusidiq
Asali: Twitter

Alkaluman da aka fitar sun nuna tsakanin Fubrairu da yau, Fidelity Bank, Ecobank da Union Bank sun samu N15.958bn, N14.703bn da N14.125bn.

Abin da bankin CBN ya rabawa rassan Stanbic Bank, Sterling Bank da Polaris bank a tsawon wannan lokaci shi ne N11.83bn, N11.242bn da N10.074bn.

Bankin nan na Wema da Unity sun samu N8.611bn da N8.586bn daga babban bankin kasar.

Kara karanta wannan

Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli'

Kudin da aka rabawa garuruwa

Idan aka yi la’akari da jihohi, Legas ce gaba da N33bn, sai FCT da aka rabawa bankunansu N27.894bn, an raba N13.1bn da N8.12bn a Ibadan da Kano.

Sauran garuruwan da suka samu sababbin kudi sosai sun hada da Maiduguri, Minna da Katsina, sai kuma Bauchi, Abeokuta, Uyo, Akure da Enugu.

'Shirin' Godwin Emefiele a Legas

Bayan APC ta lashe zaben Shugaban kasa, an samu labari cewa Gwamnan CBN yana taimakawa Jam’iyyar LP a Legas a zaben Gwamnoni da za a shirya.

Godwin Emefiele ya yi amfani da bankin CBN, ya ba ‘Dan takaran LP Naira miliyan 500 domin yin kamfe a lokacin da ake fama da karancin takardun kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng