Bayan Watanni 14 Da Rasuwa: Har Yanzu Ba’a Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Wayas Ba

Bayan Watanni 14 Da Rasuwa: Har Yanzu Ba’a Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Wayas Ba

  • Sanata Joseph Wayas, tsohon shugaban majalisar dattawa ya rasu tun a watan Disambar 2021
  • Watanni 14 bayan mutuwar Wayas, rashin kudi ya sa har yanzu ba a binne shi ba
  • Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade ya fitar da kudi tare da kafa kwamitin binne gawarsa amma sai takkadama ta shigo lamarin

Watanni 14 bayan mutuwarsa, har yanzu gawar tsohon shugaban majalisar dattawa a Jumhuriya ta biyu, Sanata Joseph Wayas, na nan an gaza binne sa, jaridar Punch ta rahoto.

Idan za ku tuna, tun a watan Disambar 2021 ne muka rahoto cewa Allah ya karbi ran Wayas a wani asibiti da ke birnin Landan.

Bayan mutuwarsa, gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya kafa wani kwamiti domin su shirya yadda za a yi jana'izarsa a nan take.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace A Sani Game Da Umar Namadi, Dan Takarar Gwamnan APC a Jigawa

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas
Bayan Watanni 14 Da Rasuwa: Har Yanzu Ba’a Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Wayas Ba Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Tsohon Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Kanu Agabi ne ke jagorantar kwamitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, bayan fiye da shekara daya, har yanzu ba a binne Wayas ba inda wata majiya ta iyalin ta bayyana cewa babu kudin da za a dauko gawarsa har ayi masa sutura, Aminiya ta rahoto.

Dansa na da bayani da zai yi wa mutane kan rashin binne mahaifinsa, dan kwamiti

Har ila yau, tsohon sakataren hukumar tsare-tsare ta kasa, Ntufam Ugbo, ya bayyana cewa a yanzu shi baya cikin kwamitin.

Yayin da yake tabbatar da cewar Gwamna Ayade ya ware kudin jana'izar nasa, Ugbo ya bayyana cewa babban dan marigayi shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas Jr shine ya fi cancanta ya yi bayanin mai ya kawo jinkirin.

Ya ce:

"Ba zai iya cewa bai da bayanin da zai bayar kan dalilin jinkiri wajen binne gawar ba. Shine babban dans, don haka shi ya kamata ya ja ragamar komai."

Kara karanta wannan

Shekarau: Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Motar Gwamna Ganduje

Martanin Wayas Jr kan rashin binne gawar mahaifinsa

Sai dai kuma, a martaninsa, Wayas Jr ya daura alhakin a kan kwamitin kan jinkiri wajen binne mahaifinsa.

Ya ce bai samu rawar ganin takawa ba sosai wajen dauko gawar mahaifin nasa kasancewar an kafa kwamitin da zai tsara jana'izar nasa.

"Batun jana'izar ba a hannunmu yake ba illa a hannun kwamitin binne gawar. Na ji an samu wasu yan takaddama dangane da kudin jana'izar. Kuma an ce wasu mambobin kwamitin sun yi murabus. Ba zan iya komawa ga gwamnan jihar ko gwamnatin tarayya ba a yanzu saboda lamuran zabe. Gwamnan ya rigada ya yi kokari sosai," cewarsa.

A wani labari na daban, kungiyar tuntuba ta arewa ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari kan abun da ka iya faruwa idan ya ki bin umurnin kotun koli kan manufar sauya kudi.

Kungiyar ta ce kin bin umurnin na iya haifar da rikici a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng