2023: CAN Ta Fada Wa Kiristoci Yan Takarar Da Za Su Kada Wa Kuri'a A Zaben Gwamnoni Da Majalisar Jiha
- Kungiyar kiristocin Najeriya CAN da umarci mabiyanta da su zabi cancanta a zaben gwamnoni mai zuwa ranar 18 ga watan Maris
- Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar reshen Jihar Niger Rev. Bulus Yohanna ya fitar ranar Lahadi
- Yohanna ya ce mabiya addinin kirista su zabi wanda ba zai nuna bambancin addini da al'ada ba, zai kuma yi adalci wajen rabon mukamai
Niger - Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen Jihar Niger ranar Lahadi a garin Minna ta umarci mabiya addinin kirista da su zabi yan takarar da suka cancanta a zaben gwamnoni da yan majalisar jiha na ranar 18 ga watan Maris.
Ta bayyana cewa dole ne yan takarar su zama masu son cigaba da zaman lafiya tsakanin al'umma, jaridar Vanguard ta rahoto.
Da Zafi-Zafi: Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili
Shugaban kungiyar CAN na jihar, Raraban Bulus Yohanna, ya bayyana a sanarwar:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
''Za a gudanar da zabe ranar 18 ga watan Maris. Ina kira ga kowa da ya zabi dan takarar da ya ke so."
Ya kara da cewa bayan tuntubar uwar kungiyar ta kasa, reshen kungiyar na jihar ya yanke cewa yan kungiyar dole su yi duba da halaye, cancanta, kwarewa da kuma tsarin kowanne dan takara kafin su zabe shi.
A cewar sanarwar shugaban kungiyar:
''Dole dan takara ya kasance mai tsoron Allah, gaskiya da kuma biyayya ga doka, adalci da kuma daidaito akan kowa.
''Dole ya zama dan takara na girmama bambancin addini da al'ada."
Halayen dan takarar da CAN ta shawarci mabiyanta su zaba a ranar 18 ga watan Maris
Ya kara da cewa dole dan takara ya zama yana son jama'a, mai tarbiya kuma samun shaidar mutane; kada ya zama dan kungiyar asiri, mai tsaurin ra'ayin addini, ko wanda ke safarar kwayoyi kuma ya zama ba shi da alaka da yan fashin daji ko yan daba.
Ya kuma bukaci masu kada kuri'a da su bibiyi ayyukan da yan takarar su kayi a mukaman da suka rike a baya.
Yan takarar dole su zama wanda za su bada tsaro, ba bambancin addini, ya kuma bawa kowa hakkinsa ya kuma yi adalci a rabon mukamai, a bukatar shugaban.
Yohanna ya ce yan takarar da aka zaba dole su bada ingantaccen ilimi da lafiya kyauta ga mutane ya kuma roki mabiya addinin kirista da suyi addu'ar gudanar da zabe lafiya.
Asali: Legit.ng