Dangote Da Wasu Manyan Kamfanoni Sun Ci Bashin Fiye Da N200bn Daga Masu Hannu Da Shuni Cikin Watanni 2
- Kamfanin Dangote Limited da MTN da wasu manyan kamfanoni sun tara kudi fiye da N200bn ta hannun takardun kasuwanci cikin wata biyu
- Kudaden da aka samu daga mutane masu hannu da shuni da hukumomi masu saka hannun jari za a yi amfani da su don tafiyar da ayyukan kamfani da fadadawa
- Wannan nasarar tara kudin da aka yi ya nuna masu saka hannun jari na kwadayin kamfanonin Najeriya
Dangote da wasu manyan kamfanonin Najeriya sun tara Naira biliyan 245 a cikin watanni biyu kacal na shekarar 2023 ta hanyar ba da takardun kasuwanci ga masu zuba jari.
An sayar da takardun kasuwancin ga masu saka hannun jari, mutane masu kudi, da sauran kamfanoni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli'
Sayar da takardun kasuwanci wata hanya ce ta kamfanoni suka saba amfani da ita don tara kudi na dan gajeren lokaci daga masu zuba hannun jari madadin ciyo bashi.
Galibi ana amfani da shi ne don biyan bashin gajeren lokaci kamar albashi, siyan kaya da sauransu.
Legit.ng ta bibiyi irinsu Kamfanin Simintin Dangote, Zenith Bank, Nigerian Breweries, MTN Nigeria, FSDH Merchant Bank Limited da wasu na cikin kamfanonin da suka tara kudi ta wannan hanyar.
DLM Capital Group Limited da Julius Berger suma sunyi amfani irin wannan hanyar don tada kudi.
Bayanan takardun kasuwanci da kamfanoni suka sayar
Ga wasu kasuwanci da aka sanar a Janairu da Fabrairu. An samu wannan bayanan ne daga rahotanni da sanarwar manema labarai, da wasu majiyoyi kwarara.
Dangote Cement ya sayar da takardar kasuwanci na N50bn
Dangote Cement ta tara Naira biliyan 50 ta hanyar takardan kasuwanci karkashin tsarinta na sayar da takardun kasuwanci na N150bn.
An fara shirin ne daga ranar Litinin 30 ga watan Janairu aka kammala a ranar Alhamis 2 ga watan Fabrairun 2023.
Kudin da aka samu za a yi amfani da su ne wurin tafiyar da harkokin kamfani.
Za a fara biyan kudin a mataki biyu; kwana 183 da 267.
Nigerian Breweries ita ma ta tara N20bn
Nigerian Breweries ita ma ta tara N20bn daga kasuwar cin bashi domin biyan wasu bukatunta a mataki uku.
Punch ta rahoto cewa biyan na farko za a yi cikin kwana 91, na biyu kuma cikin kwana 120, sai na uku cikin kwana 154.
Sauran kamfanonin da suka tara kudi ta hanyar takardun kudi daga Janairu zuwa Fabrairu
- MTN Nigeria - N125bn
- FSDH Merchant Bank Limited - N15bn
- DLM Capital Group Limited - N5bn
- Julius Berger - N30bn
Dangote ya tafi kotu kan rikicinsa da gwamnatin jihar Kogi
A wani rahoton kun ji cewa kamfanin Dangote Industries Limited ya kai kara a kotun daukaka kara ta birnin tarayya Abuja kan rikicinsa da gwamnatin jihar Kogi.
Lauyan kamfanin Dangote na son Alkali ya bada muhimmanci kan karar da ya kai gabansa.
Asali: Legit.ng