Tashin Hankali Yayin Da Aka Tsinci Magidanci Da Matarsa A Sume Cikin Gidansu Da Jinjirinsu A Mace A Ondo
- An tsinci mata da miji a sume a cikin daki da kuma jinjirin su wanda ya rasu a cikin daki a unguwar Owo a jihar Ondo
- Makwabta sun ce mutumin ya siya janareta cikin yan kwanakin nan kuma ana tunanin sun kuna janaretan kafin su kwanta barci
- Rundunar yan sandan Ondo ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce matar daga bisani ta mutu amma mijin yana asibiti
Jihar Ondo - Rundunar yan sandan jihar Ondo a ranar Asabar ta ce ta fara bincike kan mutuwar wata mata da jinjirinta cikin dakinsu a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo na jihar.
An tattara cewa an gano matar yar shekara 29 mai suna Tawa, da mijinta a sume yayin da jinjirinsu dan wata biyar ya riga ya mutu a dakin a ranar Juma'a.
Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An rahoto cewa cewa su ukun sun kwanta lafiya kalau a daren ranar Alhamis, The Punch ta rahoto.
Majiya ta magantu kan mutuwarsu
Wata majiya ta ce mata da mijin sun siyo sabon janareto yan kwanaki kafin afkuwar lamarin, kuma sun kunna janaretan a daren ranar Alhamis kafin barci, ana zargin hayakin janaretan ya kashe su.
A cewar majiyar, an same iyalan cikin mawuyacin halin a ranar Juma'a. Jinjirin su ya riga ya rasu, mata da mijin suna sume kuma an garzaya da su Cibiyar Lafiya Ta Tarayya, Owo, inda matar ta rasu, yayin da likitoci na kokarin ceto ran mijin.
Majiyar ta ce:
"Lokacin da yayan marigayiyan ta ga ba ta zo aiki ba a ranar Juma'a da rana, ta damu. Don haka ita da sauran ma'aikata suka tafi gidan ta.
"Da suka isa gidan, sun tarar kofar a rufe sai da suka balle kofar suka gano mata da mijin a sume yayin da jinjirinsu ya rasu. Sun garzaya da su FMC inda matar ta mutu amma shi mijin yana can rai a hannu Allah."
Martanin rundunar yan sanda
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar, Mrs Funmilayo Odunlami, sun tabbatar da afkuwar lamarin amma ta ce ba a san sanadin mutuwar ba kuma an fara bincike.
Kakakin yan sandan ta ce:
"Ba za mu iya cewa ga abin da ya janyo lamarin ba. Wasu na cewa hayakin janareta ne, amma an kuma ga kwalbar snipper a dakin. Watakila sun fesa a dakin kafin su kwanta. Ana dai bincike kan lamarin."
Asali: Legit.ng