Na rantse da Allah ban ɗauki ko sisin Jihar Kaduna ba, Wanda ya Ƙaryata Yazo Mu Dafa Kur'ani - El-Rufai
- A bidiyon daya zagaye kafafen sadarwa mai mintun 2 da sec 25 an jiyo Elrufai na cewa wallahi bai saci kudin jihar Kaduna ba.
- Ya kalubalanci duk wanda yace ya sata daya fito da hujja, ko da acikin kudin da ake turowa jihar ne ko cikin kudin shiga
- Elrufai yace yace bai sayi gida a Dubai ba, ko wata kasa, kuma har ya gama mulkin jihar Kaduna, gida daya ne dashi tak
Kaduna - A yayin da mulki a Najeriya yake zuwa gangarar shekaru huɗu da aka soma ƙirga a shekarar mulki ta 2019.
Yan Najeriya na cigaba da zargin gungun yan siyasa da azurta kansu tare da sace dukiyar al'umma a kowani mataki na mulki.
Bugu da ƙari, yan siyasa na cigaba da nuna yatsa a tsakanin su, kodai don faɗin gaskiya ko kuma neman tausayin al'umma domin samun kuri'a da kariya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Watakila hakan ne yasa gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna fitowa yana faɗin cewa duk wani wanda ya taɓa mulkar jihar Kaduna a baya ya fito ya rantse cewar bai ɗauki kuɗin al'umma ba kamar yadda shima zai rantse.
El-Rufai na wannan batun ne biyo bayan zayyana yadda gwamnatin sa tayi ayyuka masu nagarta ba tare da rage kuɗi ko yin ɗingushe ba a cikin kuɗin kwangilolin da ake bayar wa a lokacin mulkin sa.
A wani faifan bidiyo mai mintuna 2 da daƙiƙa 25 da Legit.ng tayi ido huɗu dashi na hirarsa da KSMC, an jiyo El-Rufai yana faɗin:
"Ban ɗauki kuɗin kowa ba, ina kalubalen duk wanda yayi shugabancin jihar nan shima ya fito, ya rantse da Kur'ani, lokacin da yayi shugabanci bai ɗauki kobo na jihar Kaduna ba Wanda ba hakkinsa ba"
Gwamnan yace ya zama gwamnan Kaduna yana da gidan zama guda ɗaya ne tak, ya gama mulki ba tare daya ƙara mallakar wani ba.
"Ina da gidana ɗaya a Ɗanja road, nagama alhamdulillahi shine gida na ɗaya, banje na gina wani gida ba, bana buƙata".
"Dukkansu kowa ya fito yazo ya kalli al'ummar jihar Kaduna yace musu bai ɗauki kudin su ba."
"Don mun san su, ba ƴaƴan ɗantata bane, ba ƴaƴan Dangote bane."
"Mun sansu tun a makaranta, a ina suka samu kuɗin yin wadannan manyan gidajen"
"Wacce sana'a suke yi, mun sani."
Ya ƙara da cewa:
"To amma mu tsarin mu, da aƙidar mu ba haka bane. Tsarin mu shine, shugaban ci amanace wacce zaka tsaya gaban Allah, ka kare kanka."
"Saboda haka ko wanni taro da sisi muke dashi, ko kuɗin shiga ne ko kuɗine daga Abuja, ko bashi muka ci, wallahi amfani mukayi dashi domin a samu ci gaban al'umma".
Gwamnan ya ƙarkare da:
"Bamu ɗauka mun saka a aljihun mu ba, ko muje mu sayi gida a Dubai, bamu da buƙatar wannan." Inji El-Rufai.
Ƴan Najeriya Sun Tattauna Akan Batun
Saboda yadda batun ya tada kura, yan najeriya nata tofa albarkacin bakin su kamar haka:
Sabo Hassan Yace:
"MashaAllah nayi maka farin ciki idan abunda ka fadi gaskiya ne. Allah Ya kara budi".
Shi kuwa Sani Hadi cewa yayi:
"Toh ayi hattara dai masu comments, shi dai ya rantse da Allah, kuma Allah ne kadai masanin abinda ke cikin zuciya. Kar mu sanya kammu cikin fitina wajen zarginsa da abinda bamu da hakikar saninsa."
Muhammad Ali Wagani cewa yayi
"Wanda ya ranse da Allah mu bamu isa mu karyata shiba, Allah yakara mana imani".
Shi kuwa Abu Shaban Tambaya yayi:
“Muna Alfahari Da Ke”: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo a Kan Murhu Kamar Babba Ya Girgiza Intanet
"Tambaya ta a wurin Nasiru naga wata jarida ta ambaceshi amatsayin Gomnonin da sukafi kudi Nigeria to wacce kasuwa rimfarsa take?."
Ku kalli faifan vidiyon anan:
Asali: Legit.ng
"Ku yafe min dan Allah": Inji Direban Motan da Yayi Kicibis da Jirgin Ƙasa a Lagos Mutum 6 Suka Mutu
Tunda fari dai an ruwaito Direban ya tunkari kan titin jirgin kasa ne dauke da mahaya ba sassautawa yayin da suke ihu suna faman ya tsaya, amma baiji ba.
Rahotanni sun ce yana sanye da abubuwan jin sauti a kunnuwan sane, yayin da yake tukin kuma yayi ƙemadagas da umarnin da masu bada hannun titin jirgin ƙasan suka yayi masa akan ya tsaya.
Direban mai suna Osinbajo, yace motar ce birkin ta ya ƙi ci shi yasa ya kasa tsayawa.
Direban da yake aiki da ma'aikatar sufuri ta jihar Lagos, tuni aka maida shi sashen binciken manya laifuka na SCID bayan tsira da yayi daga hatsarin batare da yaji ko ƙwarzane ba daga hatsarin.
Kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito, ta jiyo Direban yana faɗawa ƴan uwan sa cewar, ba laifin sa bane, laifin motar ne da birki ya kwace.
Asali: Legit.ng