Hattara: Sabuwar Hanyar Da Ƴan Yahoo Ke Kwashe Kuɗi Ta Bayyana

Hattara: Sabuwar Hanyar Da Ƴan Yahoo Ke Kwashe Kuɗi Ta Bayyana

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya ankarar da mutane kan sabuwar hanyar da ƴan Yahoo suke amfani da ita suna kwashewa mutane kuɗaɗe
  • Ta hanyar yin amfani da wayar sa, ya nunawa mutane yadda za su iya yin asarar kuɗaɗen su a asusun jihar su ba tare da sun bayyana lambobin katin ATM, lambobin sirri ko OTP ba
  • Mutane da dama a soshiyal midiya sun yaba kan wannan muhimmin bayanin da yayi inda wasu daga ciki suka tabbatar da sun taɓa samun irin waɗannan saƙon nin

Wani ɗan Najeriya mai suna Injiniya Victor, ya tona asirin wata sabuwar hanya da ƴan Yahoo suke amfani da ita wajen kwashewa mutane ƴan matsabban su.

Ya bayyana cewa da wannan sabuwar hanyar, ƴan Yahoo suna kwashe kuɗi daga asusun mutane ba tare da katin ATM, lambobin sirri ko OTP ba.

Kara karanta wannan

2023: Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Kotu Ta Jiƙawa INEC Aiki, Ta Bata Wani Sabon Umurnin Dole

Yahoo
Hattara: Sabuwar Hanyar Da Ƴan Yahoo Ke Kwashe Kuɗi Ta Bayyana Hoto: TikTok/apostletalker
Asali: TikTok

Da yake nuna yadda suke yi, ya bayyana cewa abinda ƴan damfarar ke yi shine za su tura saƙonni barkatai ga wayoyin mutane.

Victor yace suna samun lambobin wayar mutane ne ta wata manhaja ta musamman sannan mutane za su rasa kuɗin su da zarar sun bi umurnin da aka basu ko kuma suka danna kan saƙonnin da aka turo musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Injiniya Victor ya bayyana cewa bankuna basu iya yin komai akai saboda a bayyane ake yi.

Ya shawarci mutane da suka goge waɗannan saƙonnin da zarar an turo musu su a waya.

Bidiyon na sa wanda Apostle Talker ya sanya a TikTok, ya ɗauki hankula sosai, inda mutane suka yi ta magana a kan sa.

Ga kaɗan daga ciki:

Mike_bossman ya rubuta:

"Mun gode da wannan bayanin naka amma ka haɗa mu da ciwon kai. Kana ta wahalar da turanci ba gaira ba dalili."

Kara karanta wannan

Yadda Aka Mamaye Ni Aka Lalube Min Wayoyi Na a Wajen Karɓar Satifiket Ɗin lashe Zaɓe, Sanatan APC

user0511483015 ya rubuta:

"Wannan bidiyon ya taimake ni, na ga irin wannan saƙon a wayata da safe. Allah ya taimake ni na kalli wannan bidiyon."

rainatabdul283 ta rubuta:

"Na sha ganin su cikin ƴan kwanakin nan. Mun gode da tunatarwa."

Barakatt__ ta rubuta:

"Na sha samun irin waɗannan saƙonnin daga wanda ban san ko wanene ba. Tuni na goge su"

Na Dena Soyayya": Wata Ta Koka Yayin Da Masoyinta Na Intanet Ya Ziyarce Ta A Karon Farko, Hirarsu Ya Bayyana

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka bayan masoyin ta na yanar gizo ya kawo mata ziyara.

Budurwar ta bayyana wani abu da yayi mata wanda ya ɓata mata rai matuƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng