Hukumar NDLEA Ta Soma Daukar Aiki: Ta Lissafa 7 Sharruda Ga Masu Niyyar Nema
- An buƙaci sababbin waɗanda suka kammala karatu su gwada sa'ar su wajen neman aiki a hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi na NDLEA a shafinta na yanar gizo gizo
- A wani saƙo da hukumar ta sanar, tace ƴan Najeriya zasu iya nema da kwalin Sakandire, Polytechnic da kuma kwalin jami'a domin zama ma'aikatan hukumar
- Hukumar ta tabbatar da hakan ta shafin ta na Twitter ranar juma'a, 10 ga watan Maris. Inda tace kyauta ne neman ba ko sisi da za'a fitar daga aljihu
Hukumar kula da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa wacce aka fi sani da NDLEA, ta sanar da soma ɗiban ma'aikatan da suka cancanta kuma ƴan Najeriya aiki wanda ta saba yi akai akai.
Hukumar tayi wannan jan hankalin ne ranar juma'a ta shafin da take wallafa saƙonni na Twitter.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sharruda da Ka'ida
Kamar yadda hukumar tace, ɗiban ma'aikatan za'a soma shine daga 12 ga Watan Maris zuwa 8 ga watan Afrilu.
Kuma, masu nema da suka hattama Sakandire, Polytechnic, da jami'a duk zasu iya nema.
- Masu neman aikin dole ne su kasance ƴan Najeriya ne su, kuma su tabbata sun mallaki katin zama ɗan ƙasa NIN.
2. Bugu da ƙari, iya amfani da sarrafa na'ura mai ƙwaƙwalwa wani ƙarin tagomashi ne idan aka zo tantancewa.
3. Ta ce duk wanda zai nemi aiki matsayin "Superintendent" dole ne ya kasance aƙalla yakai shekara 20 kuma bai wuce shekara 35 ba.
4. Amma kuma adadin shekarun da ake ɓukata ga masu neman aikin "Narcotic Agent Cadre" da kuma "Narcotic Assistant Cadre" Shekaru 30 akeso sannan ba'a so suyi ƙasa da shekaru 18 yayin neman aikin.
5. Wajibi ne mai nema ya kasance lafiyayye kuma ya gabatar da hujjar haka daga wani asibitin gwamnati
6. Wajibi ne mai nema ya kasance yana da tsayi akalla mita 1.65 ga maza kuma 1.60 ga mata.
7. Mai nema ya kasance mai kyawun hali kuma ba'a taba kama shi da laifi ba.
INEC Zata Ɗaukaka Ƙara Kan Umurnin Kotu Na Ayi Zaɓe Da Katin Zaɓe na Wucin Gadi.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) bata amince da hukuncin da wata kotu tayi ba kan yin zaɓe da katin zaɓe na wucin gadi.
Hakan ya biyo bayan da INEC ta ce sam bata amince ba sannan zata ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba domin ƙalubalantar hukuncin da akayi mata.
Idan za'a iya tunawa dai, wata babbar kotun tarayya dai ta umurci hukumar INEC da ta bari wasu mutum biyu su yi zaɓe da katin zaɓe na wucin gadi.
Asali: Legit.ng