Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un: Allah Ya Yiwa Basaraken Abuja, Etsu Na Yaba Rasuwa
- Yanzu muke samun labarin rasuwar basaraken Abuja, Etsu na Yaba da ke yankin Abaji a birnin na tarayya
- Allah ya yiwa Alhaji Abdullahi Adamu rasuwa ne a hanyarsa ta zuwa masallaci don yin sallar Magriba a jiya Alhamis
- Dangin kusa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace za a yi jana'izarsa a ranar Juma'a da misalin karfe 9 na safe
Abaji, Abuja - Alhaji Abdullahi Adamu, wani fitaccen basaraken gargaji na Yaba a yankin Abaji na babban birnin tarayya Abuja ya kwanta dama.
Wani dangin basaraken, Shu’aibu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.
A cewarsa, marigayi Etsu na Yaba ya rasu ne a hanyarsa ta zuwa sallar Magriba a cikin masarautar tasa.
Yadda lamarin ya faru da kuma rahoton likitoci
A cewar Shu’aibu, sarkin ya yanke Jiki ne nan take, sai fadawansa suka yi gaggawar tafiya dashi asibiti domin duba abin da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, an yi rashin sa’a sarkin ya yi sallama da duniya, kamar yadda majiyar ta tabbatar..
A kalamansa:
“Yana faduwa, suka dauke shi zuwa cikin mota tare da zarcewa asibiti. Amma an yi rashin sa’a ana isa asibitin, likitoci suka ce ya rasu.”
Za a yi jana'iza a ranar Juma'a
Jaridar ta tattaro cewa, an dauki gawar dattijon basaraken mai shekaru 62 zuwa masarautar Yaba domin yin jana’izarsa da misalin karfe 9 na safiyar yau Juma’a 9 ga watan Maris.
Wannan lamari dai na zuwa ne bayan rasuwar Etsu na Kwali shi ma a babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Sha’aban Audu Nizaz, wanda ya rasu a wani asibitin kudi na Abuja a ranar 29 ga watan Disamban bara.
Allah ya yi wa ɗan Sarki a Yobe rasuwa
An shiga alhini a jihar Yobe yayin da aka samu labarin rasuwar dan Mai Martaba sarkin Gazargamu, Ibrahim Tijjani Saleh, Hakimin Laruski.
Rahoto ya bayyana cewa, basaraken ya rasu ne a sanadiyyar hadarin da auku dashi a cikin a daidaita sahu.
Mai Martaba Sakin Bade, Alhaji Abubakar Sulaiman ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Sarkin na Gazargam, Alhaji Tijjani Saleh Geidam, inji rahoto.
Asali: Legit.ng