An Kashe Jami’in ’Yan Sanda a Kokarin Dakile Harin ’Yan Ta’addan ISWAP a Borno
- ‘Yan ta’addan ISWAP sun hallaka wani dan sanda a lokacin da suka farmaki jami’ai a wani yankin jihar Borno
- ‘Yan ta’addan sun mamaye wurin da ‘yan sandan suke, inda suka saci motar ‘yan sandan suka gudu da ita
- Jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’addan ISWAP da Boko Haram a Arewa maso Gabas
Jihar Borno - An kashe wani jami’in dan sanda a yayin arangama da ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP mai aikata barna a Arewacin Najeriya, TheCable ta ruwaito.
An kashe jami’in ne a lokacin da jami’an ‘yan sanda da ke kokarin dakile harin ‘yan ta’addan na ISWAP.
A cewar rahoton kafar labarai na Zagazola Makama, ‘yan ta’addan sun kutsa wurin da jami’an ‘yan sandan suke ne cikin dare da misalin karfe 2 na Talata.

Source: UGC
Majiya ta bayyana yadda lamarin ya faru
A cewar majiya, ‘yan ta’addan sun farmaki ‘yan sandan ne ta bangarori da yawa, lamarin da ya jawo zazzafan fada.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Yan sandan sun yi kokarin dakile harin, inda suka shafe mintuna 30 suna musayar wuta, lamarin da ya kai ga ‘yan ta’addan suka tsere da motar ‘yan sanda.
A cewar majiyar:
“Jami’an sun yi nasarar sace iskan tayun motar kafin su tsere da motar.”
Matakin da ake dauka
Ya zuwa yanzu, an tura jami’an tsaron da suka bibiyi inda ‘yan ta’addan suka shiga.
Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ‘yan ISWAP din suka hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram sama da 200 a yankin Gudumbali da ke jihar ta Borno.
A bangare guda, a ranar 23 ga watan Janairu ne jami’an sojojin Operation Hadin Kai sun dakile harin ‘yan ta’addan ISWAP a kauyen Komala kusa da Maiduguri daga Dambua a jihar ta Borno.
‘Yan ta’addan Boko Haram sun ajiye makamai
A wani labarin kuma, kun ji yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka ajiye makamai bayan samun mummunan asara daga hannun abokan gabansu ‘yan ta’adda.
Ragargazar da sojojin Najeriya ke yi a yankin Arewa maso Gabas, musamman a jihar Borno na ci gaba da jikkata jin dadin ‘yan ta’adda a yankin.
Rahoto ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun mika wuya ne tare da daruruwan ‘ya’ya da matansu da suke rayuwa a daji.
Asali: Legit.ng

