Abun Mamaki: Wani Mutumi Ya Miƙe Daga Kan Keken Guragu, Ya Kama Rawa da Amarya

Abun Mamaki: Wani Mutumi Ya Miƙe Daga Kan Keken Guragu, Ya Kama Rawa da Amarya

  • An ga dirama a wurin liyafar wani aure lokacin da wani mutumi ya tashi daga kan Keken Guragu ya hau kan dandamalin rawa
  • Abun da ya ƙara baiwa mutane mamaki shi ne yadda mutumin ya miƙe da kansa kuma ya kama tiƙa rawa tare da amarya
  • Mutane sun maida martani daban-daban a Bidiyon, wasu na tantamar dama can ba gurgu bane yayin da wasu ke ganin iko ne daga Allah

Wani mutumi da ake zaton gurgu ne a kan Keken Guragu ya bar mutane baki buɗe yayin da aka ga ya yi zumbur ya miƙe a kan kafafunsa a wurin shagalin bikin aure.

Wani mai amfani da kafafen sada zumunta wanda ya wallafa bidiyon yadda abun ya faru a TikTok ya ce abun Al'ajabi ne da mu'ujiza.

Liyafar aure.
Abun mamaki a wurin biki Hoto: Barbie_princess
Asali: TikTok

A bidiyon, mutumin na zaune a kan Keken Guragu ya yi shiga mai ban sha'awa ya shiga wurin taron shagalin bikin kuma kai tsaye ya nufi wurin da Amarya take zaune.

Kara karanta wannan

An Gano Wanda Ya Haddasa Jirgin Kasa Ya Murkushe Motar Ma'aikatan Gwamnati a Legas

Da zuwansa Amarya ta ja shi zuwa tsakiyat wurin da aka tanada domin rawa, sakanni bayan fara rawar, aka ga mutumin ya miƙe zumbur ba tare da wani ya taimaka masa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga miƙe wa kan kafafunsa, Mutumin ya bi sahun amarya, ya kama tiƙa rawa kamar ba shi ne mutumin da ke zaune a kan Keken Guragu ba.

Mutane sun nuna tantama kan naƙasar mutumin, inda suka ce ba Mu'ujiza bace Wani shiri ne kawai duba da yadda Amaryar ba ta yi mamaki ba.

Duba bidiyon anan

Martanin mutane a Soshiyal midiya

Clem Mond ya ce:

"Abun dariya, ya ciri tuta a wurin bikin ɗan uwansa, akwai abun mamaki a Bidiyon nan."

the_stephanois_official ya ce:

"Akwai abun Al'ajabi, amma idan ka duba da kanka, idan bai maka aiki ba to akwai damuwa."

Emmanuelle ya ce:

Kara karanta wannan

Dumu-dumu kenan: Bidiyo mai daukar hankali na yadda barci ya kwashe yaro na tsaka da barnata Milo

"Tsohon bidiyo ne kuma ba wai gurgu bane. Ya ɗan samu haɗari a guiwarsa ne ana gab da bikinsa."

A wani labarin kuma Wani bidiyo ya ja hankalin mutane ganin yadda wani karamin yaro ya bushe da bacci yana tsaka da ɓarna

An ga yaron ya yi kaca-kaca da kwallon milo kafin daga bisa ɓarawon bacci ya yi awon gaba da hi bakinsa a wangame.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262