Wuta Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwar Kano, Ta Lakube Shaguna 19 da Masallaci

Wuta Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwar Kano, Ta Lakube Shaguna 19 da Masallaci

  • Gobara ta tashi a kasuwar Rimi kwanaki kaɗan bayan abinda ya faru a kasuwar Kurmi da ke cikin kwaryar birnin Kano
  • Sarkin Kasuwar Rimi ya ce kusan shaguna 19 sun kone da kuma wani Masallaci, ya roki gwamnati ta agaza musu
  • Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da lamarin kuma ta kai ɗauki a kan lokacin da ya dace

Kano - Wata mummunar Gobara ta lalata kusan shaguna 19 da Masallaci a fitacciyar kasuwar Rimi, da ke karamar hukumar Kano Municipal, cikin kwaryar birnin Kano.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wata gobara da ta barke ta cinye shaguna 80 a kasuwar Kurmi, wacce ba ta da tazara mai nisa da kasuwar Rimi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Taswirar jihar Kano.
Wuta Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwar Kano, Ta Lakube Shaguna 19 da Masallaci Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Da yake hira da Daily Trust, shugaban kasuwar, Alhaji Musa Tijjani Sarkin Kasuwar Rimi, ya ce suna zargin wutar ta tashi ne daga matsalar wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Ta Kwaɓe, Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ta Yi Murabus, Ta Koma APC da Dubbannin Mambobi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sarkin Kasuwar ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare kuma gobarar ta ƙona muhimman kayayyaki ƙurmus.

Ya ƙara da cewa daga cikin kayan da wutar ta ƙona kurmus har da tsarin ginin shaguna, kayan hatsi da kayan yaji da sauransu.

Ya ce:

"Mun gode wa Allah babu wanda ya rasa rai a lamarin amma mutane sun yi asarar dukiya mai ɗumbin yawa saboda shagunan sun ƙone sosai. Muna rokon gwamnati ta taimaka mana domin da yawa sun rasa jarinsu."

Wane mataki aka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin hukumar kwana-kwana ta Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce sun samu labari kuma cikin hanzari suka tura jami'ai wurin.

"Bayan mun je kasuwar, mun ga shaguna 14, Masallaci ɗaya da kuma shagunan wucin gadi 5 suna ci da wuta, dukkan su sun kone kurmus."

Kara karanta wannan

Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

"Bisa namijin kokarin jami'an mu, mun yi nasarar ceto shaguna da dama daga kamawa da wuta a cikin harabar kasuwan, ba bu wanda ya ji rauni ko ya mutu."

A cewarsa, duk da babu tabbatacin abinda ya haddasa tashin wutar, ya yi kira ga ɗaukacin al'umma su rika kashe wutar lantarki idan ba amfani zasu yi da ita ba.

Shugaban ’Yan Sanda Ya Tura Sabon CP Kano

A wani labarin kuma Sufetan yan sanda na ƙasa ya tura sabon kwamishina 'yan sanda zuwa jihar Kano bayan abinda ya faru

Hakan dai ba zai rasa alaƙa da shirin rundunar 'yan sanda na samar da ingantacen tsaro yayin zaben gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohi.

A ranar Asabar mai zuwa, 11 ga watan Maris za'a gudanar da zaben kuma Kano na ɗaya daga cikin jihohin da ake hasashen zaben zai yi zafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262