Gwamnatin Ondo Ta Yi Rabon Maganin Bera Don Yakar Cutar Zazzabin Lassa
- Gwamnatin jihar Ondo ta yi rabon maganin bera domin kashe cutar zazzabin Lassa a jihar da ke Kudu maso Yamma
- An fara rarraba wannan maganin ne a wasu kananan hukumomin jihar bisa zargin cutar ta fara ta’azzara
- Jihar Ondo na daya daga cikin jihohin da hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC tace Lassa ta fi yawa
Owo, jihar Ondo - A yunkuri da kokarin dakile yaduwar zazzabin Lassa, gwamnatin jihar Ondo ya fara rabon maganin bera don rage adadin berayin da ke yawo a jihar, Tribune Online ta ruwairo.
Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC a baya ta ayyana Ondo a cikin jerin jihohin da cutar zazzabin Lassa ya fi yaduwa a Najeriya.
Musamman, an fara rabon wadannan magungunan kashe bera ne a kananan hukumomin Owo, Akure South, Akure North, Ose, Akoko South-West, Akoko South-East da Idanre.
Dalilin raba maganin bera da abin da ake son cimmawa
Da yake magana a wajen kaddamar da taron rabon magungunan a Owo, kwamishinan lafiya a jihar, Dr. Banji Ajaka ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Akwai cibiyoyin jinya guda uku a jihar, ciki har da asibitin gwamnatin tarayya na Owo da dai sauransu don tabbatar da samun kulawar likita cikin sauki.
“Dole gwamnati ta samar da maganin bera tare da raba shi kyauta ga mazauna kana ta bukaci su yi amfani dashi yadda ya dace.”
Mun gode gwamna, basaraken gargajiya ya yi martani
A nasa jawabin, Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye ya yaba da kokarin gwamna Rotimi Akeredolu a fannin kiwon lafiya, rahoton Punch.
Ya kuma bayyana cewa, yana jinjinawa gwamnan bisa nemi hanyar magance zazzabin Lassa, inda ya kara da cewa, mutanen Owo suna sane da illar cutar.
Ya kuma yi kira ga mazauna garin da su tabbatar da ba gwamnati hadin kai ta hanyar amfani da maganin mai kashe beraye don rage yaduwar Lassa.
Annobar mashako ta kashe jama’ar Kano da yawa
A wani labarin, kun ji yadda hukumar NCDC ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ta sanadiyyar annobar mashako da ta tashi.
Wannan na zuwa ne watanni bayan da aka bayyana bullar cutar mai kisa a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.
Rahoton da muka samo ya bayyana alamomi da kuma abubuwan da cutar ke tattare dashi da kuma yadda ake kula da ita.
Asali: Legit.ng