Kotu Ta Hana Yan Sanda Kama Dan Takarar Gwamna Da Ake Nema Ruwa A Jallo, Ta Bada Dalili
- Babban kotu da ke Imo ta hana yan sanda da DSS kama Benard Odoh, dan takarar gwamna na APGA a jihar Ebonyi
- Da farko yan sandan sun ayyana nemans Odoh ruwa a jallo kan zargin da gwamnatin jihar ta masa na hannu kan kisar wani sarki a jihar
- Wasu yan daba sun kai hari suka kashe basaraken a makon da ta gabata, amma dan takarar gwamnan ya ce ba shi da hannu kan lamarin
Owerri, Imo - Babban kotu a Imo ta bada umurnin hana yan sanda da DSS kama Farfesa Benard Odoh, dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, jihar Ebonyi.
A cewar New Telegraph, kotun ta bada umurnin hana sifeta janar na yan sanda, Usman Alkali Baba da Sunday Olaleye, kwamishinan yan sanda na Ebonyi, da jami'an SSS ayyana neman Odoh ruwa a jallo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da yasa yan sanda suka ayyana neman dan takarar gwamnan jihar Ebonyi ruwa a jallo
SP Onome Onovwakpoyeya, mai magana da yawun yan sanda, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Maris, ya ayyana neman Odoh da wasu mambobi da magoya bayan APGA ruwa a jallo.
An rahoto cewa yan daba sun kashhe Igbokwe Ewa, mai sarautar gargajiya wanda ke goyon bayan Odoh.
Amma, gwamnan jihar ya zargi dan takarar gwamnan da hannu kan kisar basaraken, kuma daga bisani yan sanda suka ayyana nemansa ruwa a jallo.
Abin da ke faruwa baya-bayan nan game da APGA, Ebonyi, APC, zaben 2023, Kudu maso Gabas, Yan Sanda, Ebonyi
A lokuta daban-daban, mai fatan zama gwamnan ya musanta zargin da aka masa, yana mai cewa marigayin basaraken kamar mahaifinsa ne kuma yana goyon bayansa.
A cewar Odoh, zalunci ne da rashin hankali a alakanta shi da kisar basaraken.
Ya zargi yan sandan da hada baki da masu adawa da shi a siyasa don rage masa daman samun nasara a zaben da ke tafe ta hanyar ayyana nemansa ruwa a jallo.
Asali: Legit.ng