Masu Sayar Da Hatsi a Kasuwannin Abuja Bayyana Dalilin Da Yasa Ba Su Karban Tiransifa, Sai Tsabar Kudi

Masu Sayar Da Hatsi a Kasuwannin Abuja Bayyana Dalilin Da Yasa Ba Su Karban Tiransifa, Sai Tsabar Kudi

  • Yan kasuwa masu sayar da hatsi a wasu kasuwanni a Abuja sun ce ba su karbar tiransifa daga hannun kwastomomi
  • Wasu cikinsu sun bayyana cewa ba zai yi wu su karba tiransifa ba saboda a hannun manoman kauye suka saro kaya kuma su ba su da banki
  • Wasu cikin yan kasuwan sun ce jarin su ba shi da yawa don haka ba zai yi wu su bari kudinsu ya makale a banki ba, sun yi kira CBN ya samar da isasun kudi

FCT, Abuja - Masu sayar da hatsi a kasuwani babban birnin tarayya Abuja, ba su yarda a tura musu kudi a asusun banki daga kwastomomi, duk da tsarin rage kashe tsabar kudi na babban bankin kasa, CBN, The Punch ta rahoto.

Yan kasuwar a Nyanya, Karu, Maraba da Masaka ba su karban 'tiranfa' kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta lura a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kashe tsoffin Naira: CBN ya yi maganar da kowa ya kamata ya sani kan hukuncin kotu

Kasuwar Hatsi
Yan Kasuwar Hatsi. Hoto: Miller Mag
Asali: Facebook

A cewar yan kasuwar, suna siyan kaya kai tsaye daga manoma daga kauyuka wadanda ba su da bankuna da za a iya tura musu kudi ta hanyar zamani na 'tiransfa'.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mrs Kadirat Ibrahim, wata mai sayar da kaya a Kasuwar Nyanya, ta ce duk da kwastomomi na raguwa, dole sai tsabar kudi za ta karba.

Ta ce:

"Ina da asusun banki amma ba zan iya yi wa wadanda zan siya kaya hannunsu tiransifa ba, ba zan amince da irin wannan nau'in kasuwancin ba. Duk da kwastomomi na raguwa.
"Ba na karbar tiransifa ko POS don wadanda muke siyan hatsi daga hannunsu manoma ne na kauye kuma da tsabar kudi muke biyan su, saboda ba su da banki."

Wata mai sayar da hatsin a kasuwar Maraba, Mr Ismaila Abu ya ce shima ba ya karbar kudi ta hanyar zamani idan ya sayar da kaya.

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

Ya ce:

"Jari ne bashi da yawa kuma ba na son a rike min kudi a banki.
"Ina bukatar tsabar kudi na a hannu, don in samu kudin da zan iya siyan kaya in cigaba da kasuwanci na.
"Ba ni da asusun banki, amma ba zan iya zuwa in bude yanzu ba. Zan jira sai wannan wahalhalun a banki ya kare."

Wani dan kasuwa mai sayar da hatsi a kasuwar Garki, Mr Ayo Ade ya yi kira ga CBN ta samar da isasun takardun kudi ga mutane saboda masu kananan kasuwanci su cigaba da harka.

An Kirkiri Canjin Kudi Ne Don Durkusar Da Tattalin Arzikin Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta yi ikirarin cewa an hana bankuna kudi ne don kawo cikas ga tattalin arzikin jihar Kano.

Muhammad Garba, kwamishinan watsa labarai na Kano, ya ce CBN ya yi kwana hudu bai bawa bankunan jihar kudi ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Bullo Yayin da Bankuna Suka Fara Zuba Tsoffin N500 da N1000 a ATM

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164