Yanzu Nan Shugaban APC Ya Shiga Ganawa da Gwamnonin Jam’iyyar a Abuja
- Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya shiga ganawa da gwamnonin jam’iyyar da kuma ‘yan takarar gwamna duk dai na jam’iyyar
- Ana kyautata zaton ganawarsu za ta shafi nasarar jam’iyyar ne a zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar 11 ga watan Maris
- A zaben shugaban kasa da aka yi, jihohi da yawa na APC sun samu tsaiko yayin da jam’iyyun adawa suka lashe zabe a can
FCT, Abuja - Gwamnonin jam’iyyar APC a Najeriya sun shiga wata ganawa da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu gabanin zaben gwamnoni a ranar 11 ga watan Maris.
Ganawar an ce tana faruwa ne a yanzu haka a hedkwatar jam’iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Baya ga Adamu, akwai mambobin kwamitin ayyuka (NWC) na jam’iyyar a ganawar da ke tafe yanzu haka.
Yadda zaben shugaban kasa ya kasance a Najeriya
Da yawan gwamnonin da ake ganawa dasu suna neman a sake zabansu ne a karo na biyu a zaben ranar 11 ga watan Maris.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jam’iyyun adawa sun mamaye wasu jihohi a zaben 25 ga watan Faburairu da ya gabata, lamarin da ya razana wasu gwamnonin.
Jihohin da jam’iyyun adawa suka mamaye a zaben makon jiya sun hada da Legas, Kano, Kaduna, Katsina, Nasarawa da kuma Filato.
Ana kyautata zaton cewa, za a tattauna nasara da makomar jam’iyyar a zaben na ranar Asabar mai zuwa.
Wadanda suka halarci taron
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da sakataren jam’iyyar na kasa, Iyiola Omisore da mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar gwamnan APC a Delta, Sanata Ovie Omo-Agege.
Hakazalika, akwai ‘yan takarar gwamna a jihohin Rivers da Bauchi; Tonye Cole da Abubakar Sadiq, tsohon shugaban hafsun sojin sama, New Telegraph ta tattaro.
Daga gwamnonin kuma, akwai gwamna Atiku Bagudu na Kebbi, Abubakar Badaru na Jigawa da Bello Matawalle na jihar Zamfara.
Jam'iyyar APC ta samu karuwa a jihar Adamawa yayin da dan takarar gwamnan jam'iyyar Labour ya bayyana janyewa daga takara.
Oumba ya ce, Binani na da ra'ayi irin nasa, don haka ya janye daga takara ya kuma marawa Binani baya.
Asali: Legit.ng