Mata Yar Shekaru 52 Ta Rasu Yayin Rikici Da Wata Matashiya Kan Rijiya

Mata Yar Shekaru 52 Ta Rasu Yayin Rikici Da Wata Matashiya Kan Rijiya

  • Wata mata mai suna Medinat Aliu, yar shekara 52 ta riga mu gidan gaskiya biyo bayan rikici da wata matashiya a Ondo
  • Rahotanni sun bayyana cewa Medinat ta gargadi wata yarinya ne ta rufe kanta kafin ta diba ruwa a rijiya, hakan ya janyo rikici tsakaninsu
  • Daga cacar-baki, yarinyar ta bangaje Medinat kuma ta fadi kasa daga bisani ta rasu, yan sanda sun ce an kama wacce ake zargi

Jihar Ondo - Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Ondo ta ce ta kama wata yarinya yar shekara 16 kan zargin tura wata mata yar shekaru 52, Medinat Aliu, ta fadi kasa ta rasu a Isolo, jihar Ondo.

Punch Metro ta tattaro cewa a ranar da abin ya faru, marigayiyan da wacce ake zargin suna cacar-baki ne kan wani abu da ya shafi rijiya a unguwar.

Kwamishinan yan sandan Ondo
Kwamishinan yan sandan Ondo, Oyediran Oyeyemi. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Wata majiya daga unguwar ta ce cacar-bakin ya yi sanadin dambe, a yayin hakan, matashiyar aka ce ta tura Aliu kuma ta fadi ta ce ga garin ku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar ta ce:

"Rikicin ya samo asali ne yayin da wacce ake zargin a unguwar tunda farko ta fara diban ruwa daga rijiyan ta yi wanka. Marigayiyar ta lura wacce ake zargin bata rufe kanta ba sai ta fada mata ta rufe kanta.
"Wannan ne ya janyo rikici. A yayin da marigayiyar ta yi kokarin janye wacce ake zargin daga rijiyar, wacce ake zargin ta tura Aliu kuma ta fadi daga bisani ta rasu."

Martanin rundunar yan sandan jihar Ondo

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ondo, ta aka tuntube ta, ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta kara da cewa an fara bincike.

Kakakin yan sandan ta ce:

"An tura binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka na yan sanda domin zurfafa bincike."

Amma, an tattaro cewa tuni an yi wa marigayiyar jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Dan sanda ya jibgi likita a Kwara don ya duba matarsa ba tare da izininsa ba

Kungiyar likitoci da likitocin hakori a babban asibitin garin Ilorin a jihar Kwara sun janye aiki na kwana biyu biyo bayan zargin cin zarafin daya cikin mambansu.

The Punch ta rahoto cewa wani dan sanda ne ya lakada wa likita a asibitin duka saboda wai ya duba matarsa ba tare da izininsa ba.

Mutumin ya ce hakan babban laifi ne kuma abin ki a al'adarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164