An Kashe Mutane 50, An Raunata Da Dama, An Kona Gidaje Yayin Hare-Hare A Binuwai
- Wasu da ake zargin makiyaya ne masu bindiga sun halaka a kalla mutane 50 a fiye da garuruwa 12 a Binuwai cikin mako daya
- Wata majiya daga daya daga cikin garuruwan da abin ya shafa ya ce harin ya faru ne bayan kammala zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya
- Alhaji Ibrahim Galma, shugaban Miyetti Allah na Binuwai ya ce zargin kwace wa makiyaya shanunsu da aka yi ne ya janyo rikicin da kashe-kashe
Binuwai - Daruruwan mutane a karamar hukumar Kwande na jihar Binawai sun tsere garinsu saboda tsoron hari da wasu da ake zargin makiyaya ne masu bindiga da suka kai hari a fiye da garuruwa 12 cikin mako guda da ya wuce suka halaka manoma 50.
Leadership ta tattaro daga mutanen garin cewa makiyayan sun kai hari a garuruwan kuma sun kashe fiye da mutane 50 yayin da dama sun jikkata tare da kona gidaje da rumbu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Harin ya fara ne daga bayan zaben shugaban kasa da yan majalisa a garuruwa a kalla 12 na Moon, Mbaikyor, Mbadura Ilyav, Ugbe, Iyon, Ityuluv, Injov Tyopaver, Kendev, Maav da wasu.
Wani a yankin da ya ce sunsansa Tersur, ya ce makiyayan sun fara harin ne daga Moon sannan suka tafi sauran garuruwan suka fatattaki mutane daga gidajensu.
Kakakin Operation Whirl Stroke, D.O. Oquah, ya fada wa Leadership cewa kwamandan rundunar, Manjo Janar Kelvin Aligbe, a jiya ya yi taro da masu sarautar gargajiya da shugabannin Miyetti Allah a kan yadda za a warware matsalar.
Kuma, tsohon shugaban karamar hukumar Kwande, Bem Tseen, ya fada wa wakilin majiyar Legit.ng cewa ya rasa yan uwansa uku a harin.
Ya ce:
"Muna gida lokacin da wadanda ake zargin makiyaya ne suka kawo hari a garuruwan mu ta wurare daban-daban. Muna da iyakoki da Kamaru, Jihar Taraba da Karamar hukumar Katsina-Ala.
"Suna kai wa mutanen mu hari daga bangaren Abande Anwase, an kashe da dama an kuma raba wasu da muhallansu. Daga bangaren Taraba, kusa da Kashimbila, suna kai hari suna halaka mutanen mu. An kashe da dama. Ana cikin rudani a karamar hukumar Kwande a yanzu da muke magana."
Sakataren Miyetti Allah na jihar Binuwai, Alhaji Ibrahim Galma ya ce makiyaya sunyi rikici da manoma a yankin hakan ya janyo kashe-kashen kan zargin kwace dabobinsu.
Gwamna Ortom na Binuwai ya ce makiyaya ne suka kai masa hari
A wani rahoton, kun ji Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce makiyaya ne suka kai wa tawagar motocinsa hari, TVC ta rahoto.
Ya yi ikirarin cewa maharan sun rika bin tawagarsa a baya-baya ne har sai da suka kai bakin wani rafi lokacin da ya fito yana tafiya a kasa.
Asali: Legit.ng