Zaben Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya: Yan Sanda Sun Kama Fiye Da Mutum 203 Kan Laifukan Zabe

Zaben Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya: Yan Sanda Sun Kama Fiye Da Mutum 203 Kan Laifukan Zabe

  • An kama a kalla mutane 203 da laifuka daban-daban yayin zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023
  • Usman Alkali Baba, Sufeta Janar na yan sandan Najeriya ya tabbatar da hakan yayin wani taro a hedwakatar yan sanda a Abuja
  • Shugaban yan sandan ya ce an kwato bindigu da sauran makamai hannunsu, kuma ana kan bincike kafin daga bisani su fuskanci hukunci

FCT, Abuja - Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, IGP, Usman Alkali Baba ya ce an kama mutane da ke saba dokokin zabe a zabukan shugaban kasa da majalisar tarayya da aka kamalla, The Nation ta rahoto.

Baba ya yi magana ne jiya lokacin da ya yi taro da manajoji na musamman na yan sanda da suka hada da DIGs, AIGs, Kwamishinonin yan sanda, CPs, da dukkan shugabannin tawagan bincike da ayyuka na rundunar a dakin taro na Goodluck Jonathan Peacekeeping Hall a hedkwatar yan sanda, Abuja.

Kara karanta wannan

Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya

IGP Usman Baba
Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, a wurin taro. Hoto: Rundunar Yan Sandan Najeriya
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"A kokarin ku na tabbatar da doka da oda yayin zabe, kun yi nasarar kawo daidaito, ceto ma'aikatan INEC da mutane da dama da ake yi wa barazana, tsare kayan zabe masu muhimmanci, kwato abubuwa, ciki da bindigu da makamai, da kama masu laifukan zabe.
"A hakan, cikin kimanin korafi 185 da yan sanda suka amsa yayin zabe, an kama jimillar mutum 203 da ake zargi da laifukan zabe daban-daban, yayin da an kwato a kalla bindigu 18 daga hannun yan daban siyasa yayin zaben.
"Ana matakai daban-daban na bincikarsu a rundunar yan sandan, kuma ina baku tabbacin cewa nan gaba za a kammala sannan a mika su sashin shari'a na INEC don hukunci."

Alkali ya yaba wa yan sanda kan yin aiki mai nagarta yayin zaben

IGP na yan sandan ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Zaben 2023: A Yayin Da PDP Da LP Suka Garzaya Kotu, SDP Ta Ce Ta Yarda Da Nasarar Tinubu

"Ana iya fahimtar jajircewa da kuka yi duba da cewa a karon farko a tarihin zaben kasarmu, galibi ba a alakanta yan sanda daga zargin da aka saba yi yayin zabe ba.
"A maimakon hakan, mun samu yabo da kwarin gwiwa daga masu sa ido kan zabe na gida da kasashen waje. Tawagar masu sa ido kan zabe na AU da ECOWAS sun jadada hakan da wasu masu sa ido na kasashen waje masu nagarta."

Shugaban yan sandan ya kara da cewa an samu nasarar ne saboda shiri, horaswa da mayar da hankali kan walwalar yan sandan aka yi tunda farko, wanda ya dace da alkawarin Shugaba Buhari na yin zabe na adalci kuma mai tsafta a 2023, Leadership ta rahoto.

Ya zaburar da yan sandan su kara kwazo da kaimi a wurin aiki.

A wani rahoton kun ji cewa an bada belin Honarabul Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya.

Kara karanta wannan

Kaico: An gurfanar da matashi a Arewa bisa zargin satar hula da kayan sakawa

An kama jigon na jam'iyyar APC ne kan zarginsa da hannu a kisar wasu mutane yayin zaben shugaban kasa da yan majalisu da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164