“Da Yanzu Na Zama Yar Gidan Magajiya”, Jarumar Fim, Omotola Jalade Ta Magantu
- Fitacciyar jarumar Nollywood, Omotola Jalade ta bayyana yadda ta kusa shiga harkar karuwanci a rayuwarta
- Omotola ta ce mutuwar mahaifinta tana matashiya yar shekaru 13 ya sa bata da tausayi saboda bata yi alhinin rashinsa ba
- Jarumar fim din ta ce ta kusa shiga karuwanci saboda ta kagu ta ga ta zama hamshakiya ta kowani hali
Shahararriyar jarumar nan ta masa'antar shirya fina-finan kudu ta Nollywood, Omotola Jalade-Ekeinde, ta bayyana yadda ta kusa fadawa harkar karuwanci don dogaro da kai yayin da take tasowa, rahoton Vanguard.
A wata hira da ta yi da wata yar jarida, Chude Jideonwo, Omotola ta bayyana yadda mahaifinta ya mutu lokacin da take da shekaru 13.
Jarumar fim din ta bayyana mutuwar mahaifinta a matsayin abun bakin ciki da ya jefata cikin wani hali na radadi.
Yadda rayuwata ta kasance bayan mutuwar mahaifina, Omotola ta yi bayani
Omo Sexy kamar yadda ake mata inkiya ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ina ganin komai ya faru a yau, mai kyau ko mara kyau ne saboda mutuwar mahaifina, ya tabani sosai, saboda ban yi alhinin mahaifina ba.
"Na fahimci cewa ni kadai ce diyarsa na tsawon lokaci kuma akwai shakuwa sosai tsakanina da mahaifina, ya kasance manajan wani gidan rawa a Lagas a wancan lokacin, manyan mutane da dama na zuwa wajen saboda haka na fara hulda da manyan mutane tun ina karamar yarinya.
"Lokacin da nake da shekaru 13, sun zo daukata daga makaranta, na san wani abu ya faru sannan na roki Allah yasa babu abun da ya samu mahaifina. Da na isa gida, sai na lura mahaifina ya mutu, don haka shiga wannan yanayi, na rasa ya zanyi ban san yadda nake ji ba, kawai na yi shiru amma yanzu da na kara girma, ina ganin na fahimci komai. Don haka na zama mara rauni kuma abun ya taba ni har yanzu.
Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya
"Babu abun da wani zai fada mani da zai girgiza ni, ina da karfin gwiwa akaina sosai kuma bana tsoron kowa. Bana tsoron rayuwa, shakka babu da na zama karuwa a yau, na kagu na yi koma menene kuma nace gara na bayar da jikina da wani ya rabani da kanina."
Daily Trust ta rahoto cewa tun bayan fara fim dinta a 1995, jarumar ta yi fina-finai sama da 300 wanda aka ci kasuwarsu ba da wasa ba.
Ni da aure har abada, Matar aure ta koka
A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya ta koka kan kalubalen da take fuskanta a gidan aurenta, ta ce ita da sake aure har abada.
Asali: Legit.ng