Bayan Cin Bashi Da Siyar Da Kadarori Domin Komawa Ƙasar Waje, Wasu Ma'aurata Sun Koma Cizon Yatsa

Bayan Cin Bashi Da Siyar Da Kadarori Domin Komawa Ƙasar Waje, Wasu Ma'aurata Sun Koma Cizon Yatsa

  • Wata mata ƴar Najeriya da iyalanta sun ci ɗumbin bashi sannan suka siyar da kadarorin su domin komawa ƙasar waje tare da fatan samun ingantacciyar rayuwa
  • A lokacin da suka isa UK, sai matsala ta fara kunno kai, lokacin da ta fahimci cewa sai ta nemi izni kafin ta samu damar fara aiki
  • Ta shiga cikin halin ƙaƙani kayi yayin da abubuwa ta ko ina suka rincaɓe mata. Ta kowane ɓangare ta duba ba sauƙi, tayi nadamar tafiyar da tayi

Wata mata mai suna (@gloriaotikor1) ta bayar da labarin yadda wasu ma'aurata ƴan Najeriya masu ƴaƴa biyar suka tsinci kansu cikin wani hali a UK.

Ma'auratan dai sun ci bashin miliyoyin kuɗaɗe, sun siyar da gidan su da motar hawa domin kawai su bar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"CBN ne Kawai Zai Bamu Umarni Akan Tsofaffin Kuɗi Na N500 Da N1000" - Bankuna

Mata da miji
Bayan Cin Bashi Da Siyar Da Kadarori Domin Komawa Ƙasar Waje, Wasu Ma'aurata Sun Koma Cizon Yatsa Hoto: iStock, Shutterstock, BBC
Asali: UGC

Sun shiga ƙasar Ingila da bizar karatu ta matar. Bayan ta isa can sai ta fahimci sai ta nemi bizar neman aiki idan ta kammala karatu, kafin ta samu dama tayi a ƙasar, wanda hakan ba ƙananan kuɗi zai cinye ba.

A cewar labarin, waɗanda suka bata bashin kuɗi a nan gida Najeriya sun yi ta kiranta suna tunanin tana isa zata biya su kuɗaɗen su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mijinta wanda yake yin aiki, da ƙyar yake iya ɗaukar nauyin ɗawainiyar su domin akwai kuɗin haya da yaran da ake ciyarwa. Gashi har yanzu matar ta kasa kammala biyan kuɗin makarantar ta.

A yayin da take labartawa ƙawarta halin da take ciki, ta bayyana cewa da tasan haka abubuwan suke da bata yi ƙoƙarin komawa ƙasar waje ba.

Ga kaɗan daga cikin abinda mutane ke cewa akan bidiyon:

Kara karanta wannan

Shirin Ya Kwance: Amarya Ta Karye Ana Saura Kwana Kaɗan Biki, Ta Je Wajen Biki a Keken Guragu

Adekoya Adeniran ya rubuta:

"Doka ta farko! Kada ka fara siyar da kadara domin tafiya ƙasar waje! Kada ka kuskura"

Evolak ya rubuta:

"Samun ingantacciyar rayuwa ba ƙasar waje bane, inda Allah ya ƙaddaro maka ne."

flikky ta rubuta:

"Meyasa za su tafi da yara biyar a lokaci ɗaya;"

peaches ta rubuta:

"Kaga dalilin da ya sanya nake cewa Canada tafi UK a fannin karatu.

user5122196360123 ya rubuta:

"Kuskuren su shine tafiyar da suka yi tare."

Bayan Kammala NYSC, Matashiyar Budurwa Ta Shilla Ƙasar Waje, Bidiyon Ta Ya Yaɗu

A wani labarin na daban, wata.matashiya ta koma.ƙasar waje tana kammala yiwa ƙasa hidima (NYSC) a Najeriya.

Ana ƙara samun yawaitar matasan dake ficewa daga ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Tags: