Jam’iyyar Labour Ta Ja da Baya, Ta Marawa Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Rivers
- Jam’iyyar Labour ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya
- An samu tsaiko a jam’iyyar Labour, inda ‘yan takarar gwamna biyu ke kai ruwa rana kan waye zai yi takara a wannan shekarar
- A jihar Adamawa, an samu dan takarar gwamnan Labour da ya bayyana janyewa daga takara tare da marawa APC baya
Jihar Rivers - Jam’iyyar Labour reshen jihar Rivers da kungiyar gangami ta Obi-dient Movement sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar gwamnan PDP a jihar, Sim Fubara a zaben 11 ga watan Maris.
Shugaban jam’iyyar Labour na jihar, Dienye Pepple ne ya bayyana hakan, inda ya ce shawarin ya zo ne duba da samar da daidaito da adalci a jihar, The Nation ta ruwaito.
Pepple, wanda ya jagoranci sauran shugabannin jam’iyyar don marawa Fubara a Fatakwal ya bayyana cewa, mazabarar Fubara ta Kudu maso Gabas har yanzu bata samar da gwamna ba a Rivers.
Ya ce, dukkan ‘yan jam’iyyar Labour sun yanke shawarin kada kuri’unsu ga dan takarar gwamnan a zaben mai zuwa don ci gaban jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rikicin cikin gida a jam'iyyar Labour
Kafin bayyana goyon bayanta ga dan takarar na PDP, an samu cece-kuce a reshen jam’iyyar a jihar, rahoton TheCable.
A baya-bayan nan, Fafaa Princewill ya ayyana kansa a matsayin dan takarar gwamna duk da kuwa da hukumar zabe ta INEC ta amince da Itubo Beatrince a matsayin sahihiyar ‘yar takarar gwamna a LP.
Mabiya bayan Princewill sun yi ikrarin cewa, an mika sunan wanda suke goyon baya ga INEC bayan hukuncin kotu a ranar 2 ga watan Faburaitu.
A bangarenta, Itubo ta yi watsi da ikrarinsu, inda tace har ila yau ita ce sahihiyar ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar ta Labour.
Dan takarar Labour ya janyewa Binani a Adamawa
A wani labarin, kunji yadda dan takarar gwamnan jam’iyyar Labour ya bayyana janyewa daga takara tare da marawa ‘yar takarar gwamnan APC baya.
Umar Otumba ya ce, zai yi aiki tare da Aisha Ahmed Binani domin ci gaban jihar Adamawa, kamar yadda rahoto ya bayyana.
Ya zuwa yanzu, jam’iyyun siyasa na ci gaba da hada kai don tabbatar da sun sun cimma manufa a zaben bana.
Asali: Legit.ng