"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

  • Tuni dai jam'iyyu adawa suka fitar da wata sanarwa dake nuni da Gwamnatin Kano na Shirin yin maguɗin zaɓe.
  • Ita kuma Gwamnatin jihar Kanon tace jam'iyyar NNPP ce ke shirin kitsa rigima da lalata fasalin zaɓen gwamnoni da za'ai.
  • A yayin da hukumar ƴan sandan jihar Kano ta bakin kakakin ta, SP Haruna Kiyawa ta magantu, cewa zata zama yar tsaka-tsaki wajen adalci.

Siyasar jihar Kano na cigaba da ɗaukan sabon salo tun bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya.

A cikin irin salon da take ɗauka ne, gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwabnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Tasha alwashin kawo tasgaro ga duk wani motsi da jam'iyyar NNPP Zatayi maras kyau yayin zaɓen dake zuwa na Gwabnoni da yan majalisu a jihara ranar 11 ga watan Maris 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Faɗi Aikin da Yake Yayin da Atiku da Jiga-Jigan PDP Suka Fara Zanga-Zanga a Abuja

Kwankwaso
Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba - Gwamnatin Kano
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin ta fitar da sanarwar hakan ne ranar Litinin data gabata ta hannun kakakin gwamnatin, Malam Muhammadu Garba wanda yake Kwamashinan labarai na jihar.

Muhammdu Garba yace, gwamnati dole ta sanar da jama'a haka saboda muhimmancin al'amarin, a cewar sa:

"... suna so suyi amfani da zaɓen wajen cin ribar rikicin da suke so su haddasa wanda ka iya kawo cikas ga zaɓen gwamna da za'ai da kuma na yan majalisar jihohi".

Kwamishinan yace sun samu rahoton shirin da jam'iyyar NNPP take na lalata sakamakon zaɓen da za'ai ta hanyar kawo rikici, kwace akwatuna, maguɗi da tada zaune tsaye.

Garba yayi nuni da cewar, ko a shekarar 2019, yan adawan sunyi maguɗi mai muni musamman a ƙananan hukumomi dake wajen jihar.

Kwamishinan yayi zargin cewa ko a wannan lokacin, yan jam'iyyar NNPP sunyi shirin aikata wannan tuggun zaɓen ta hanyar amfani da yan jagaliyar siyasa domin tada zaune tsayen da zai basu damar yin maguɗi.

Kara karanta wannan

Ku taimake ni: Gwamnan PDP ya yi murya kasa-kasa, ya roki mata alfarma a zaben ranar Asabar

Yayi kuma yi nuni da cewa, saƙon da ƴan adawar suka aika ga yan jaridu, ba komai bane face ɓadda bami domin kitsa abinda suka shirya aikatawa.

Ya bada tabbacin cewa, gwamnati zatai duk me yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya ya wanzu a jihar.

Yayi kira ga masu ruwa da tsaki, musamman akan aikin tsaro dasu tsagulo mutum ko wata kungiyar datayi ƙoƙarin kawowa mutane tasgaro wajen kaɗa ƙuria.

Kamfanin dillancin Najeriya (NAN) ya ruwaito yadda NNPP ta sanar da mutane yadda APC ke shirin musgunawa masu kada kuri'a a ranar zaɓe.

Kamar yadda jigo a jam'iyyar NNPP Baffa Bichi yace, akwai buƙatar shigowar jami'an tsaro cikin harkar zaɓe domin tabbatar da adalci da demokradiyya sahihiya.

Bappa Bichi, ya roƙi INEC da tayi adalci a dukkan lamurran ta.

Shima kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa yace, hukumar yan sanda zata tabbatar bata ɗauki tsagi ba yayin gudanar da zaɓen kamar yadda Vanguard ta ruwaito

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1

Ana Ci Gaba Da Layi Don Samun Tsabar Kudi, Kwastamomi Na Baiwa Jami’an Banki Cin Hanci

Har yanzu ana fuskantar cunkoso yayin gudanar da hada-hadar kuɗi a bankuna a faɗin kasar nan.

Saboda matsalar karancin tsabar kudi, kwastamomi sun koma ba ma'aikatan banki cin hanci domin samun hanyar shiga cikin sauki.

Mutane sun koka kan yadda suke shafe awanni a kan layi ba tare da kudi ya kai kansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida