INEC Za Ta Ba Zababbun Sanatoci 98 Da ’Yan Majalisar Wakilai 325 Takardun Shaidan Lashe Zabe

INEC Za Ta Ba Zababbun Sanatoci 98 Da ’Yan Majalisar Wakilai 325 Takardun Shaidan Lashe Zabe

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akalla zababbun sanatoci 98 ne za a ba takardun lashe zabe daga hukumar INEC
  • Hakazalika, za a ba zababbun ‘yan majalisun tarayya 325 takardun shaidan lashe zaben duk dai a yau Talata
  • An yi zabe a Najeriya a ranar 25 ga watan Faburairu, har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana kan sakamako

FCT, Abuja - Zababbun sanatoci 98 da ‘yan majalisun tarayya 325 ne za su karbi takardun shaidan lashe zabe a bana a ofishin hukumar zabe ta INEC da ke Abuja.

A cewar rahoton jaridar The Nation, a yau Talata 7 ga watan Maris ne za a ba wadannan zababbun ‘yan siyasa takardun a hedkwatar INEC.

Sune ‘yan takarar da aka ayyana sun ci zaben da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Faburairun da ya wuce, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

INEC za ta ba da takardun shaidan lashe zabe ga wasu 'yan siyasa
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmud Yakubu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Idan baku manta ba, an yi zabe a Najeriya, inda aka samar da Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda za a ba takardun shaidan lashe zabe

Sanatocin da aka zaba sun fito ne daga jam’iyyu bakwai na Najeriya da suka hada da APC, APGA, Labour, NNPP, PDP, SDP da kuma YPP.

Jam’iyyar APC ta samu sanataoci 57, APGA 1, Labour 6, NNPP 2, PDP 29, SDP 2 da kuma YPP mai sanata 1, New Telegraph ta tattaro.

A bangaren majalisar wakilai ta tarayya, jam’iyyar APC na da zababbun ‘yan majalisu 162, ADC 2, APGA 4, Labour 34, NNPP 18, PDP 102, SDP 2 sai kuma har ila yau YPP mai dan majalisa 1.

Da yawan ‘yan majalisun tarayyar da za su shiga majalisar a bana sabbin zuwa ne, kamar yadda rahoto ya bayyana a jiya.

A cewar rahoton, akwai tsoffin gwamnoni 11 da kuma babban shugaba, tsohon mataimakin gwamna da kuma mataimakin gwamna mai ci a cikin zababbun sanatocin.

Tsoffin gwamnonin da mataimakan gwamnan da suka ci zabe zuwa majalisar dokoki ta kasa

1. Adams Osiomhole (Edo)

2. Orji Uzor Kalu (Abia)

3. Godswill Akpabio (Akwa Ibom)

4. Seriake Dickson (Bayelsa)

5. Dave Umahi (Ebonyi)

6. Danjuma Goje (Gombe)

7. Ibrahim Hassan Dankwambo (Gombe)

8. Ibrahim Shekarau (Kano)

9. Adamu Aliero (Kebbi)

10. Gbenga Daniel (Ogun)

11. Ibrahim Gaidam (Yobe)

12. Idiat Adebule (Mataimakin gwamnan Legas)

13. Ipalibo Banigo (Mataimakin gwamnan Rivers)

A makon da ya gabata ne aka ba Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shettima shaidar lashe zaben bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.